Ruguntsumi a Kano yayin da Aminu Ado Ya Kalubalanci Sanusi II kan Hawan Sallah

Ruguntsumi a Kano yayin da Aminu Ado Ya Kalubalanci Sanusi II kan Hawan Sallah

  • Rikicin masarautar Kano ya ɗauki sabon salo yayin da Sanusi II da Aminu Bayero ke shirin gudanar da hawan salla daban-daban a jihar
  • Aminu Bayero ya aike wa 'yan sanda wasiƙar cewa zai gudanar da Hawan Daushe da Nassarawa, duk da shari’ar da ke gudana
  • Jama’ar Kano na nuna fargaba, yayin da wasu dattijai da matasa ke bayyana damuwarsu kan yiwuwar rikici a lokacin hawan salla

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Al’ummar Kano sun shiga damuwa bayan da sarakunan masarautar biyu, Sarki Sanusi II da Aminu Ado Bayero, ke shirin gudanar da hawan salla daban-daban.

Tsagin sarakunan na 15 da na 16 sun ce za su yi hawan salla, duk da rikicin shari’a da ke tsakanin su a kotu.

Aminu Ado da Sanusi II za su yi jawabi sallah a Kano
Bayan sanarwar Gwamna Abba Kabir, Aminu Ado Bayero ya shirya hawan salla a Kano. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Masarautar Kano.
Asali: Twitter

Hawan salla: Aminu Ado ya fitar da sanarwa

Kara karanta wannan

Bayan barazanar dokar ta baci a Kano, Aminu Ado Bayero ya gana da Wike

Aminu Bayero ya fitar da wasiƙa ta hannun sakatarensa Abdullahi Kwaru, inda ya bayyana shirin gudanar da hawan salla a bana, cewar rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tura wasiƙar zuwa ga Kwamishinan ’Yan Sanda, inda aka bayyana niyyar yin Hawan Daushe da na Nassarawa bayan Sallah.

Aminu Bayero ya ce hawan na bana yana da matuƙar muhimmanci gare shi domin yana cika shekaru biyar a matsayin Sarki.

Ba a gudanar da hawan salla a baya-bayan nan ba saboda tsoron rikici tsakanin mabiyan Sanusi II da na Aminu Ado Bayero.

Aminu Ado zai yi hawan salla da ake fargabar hakan zai jawo rigima
Ana fargabar abin da ka iya biyo baya yayin da Aminu Ado ya shirya hawan salla kaar Sanusi II a Kano. Hoto: Masarautar kano, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Mene gwamnatin Kano, Sanusi II suka ce?

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci Sanusi II da ya shirya gudanar da hawan salla a matsayin Sarkin Kano na 16.

Sanusi II da gwamnatin jihar ba su ce uffan ba kan wasiƙar Aminu Ado Bayero, kuma rundunar ’yan sanda ba ta fitar da bayani ba, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mummunan rikici ya barke, gwamna ya tara sarakuna bayan sanya dokar hana fita

Jama’a na nuna damuwa kan yadda rikicin ke ƙara tsananta, musamman da ganin an yi shiru daga mahukunta da bangarorin biyu.

Wani dattijo Haladu Bello mai shekaru 78 ya ce yana da fargaba, yana kuma ganin hawan na bana na iya janyo rikici a cikin al’umma.

Dattijon ya ce:

“Na sha ganin hawan salla iri-iri, amma wannan na bana yana da ban tsoro sosai.
“Shugabanni na watsi da hatsarin da ke tunkaro al’umma, wannan abu ne mai tayar da hankali."

Wani matashi Alhaji Usman Shehu, ya ce rikicin cikin gida ne, kuma bai kamata a jefa jama’a cikin tsoro da damuwa ba.

Ya ce:

“Kullum cikin fargaba muke, wannan abu ne da ya kamata shugabanni su dakatar da shi domin zaman lafiya."

Yayin da bikin salla ke ƙaratowa, jama’a na ci gaba da fargabar abin da ka iya faruwa idan bangarorin biyu suka ci gaba.

Aminu Ado Bayero ya gana da Wike

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya gana da ministan Abuja, Nyesom Wike a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers.

Basaraken ya gana da Wike ne kafin halartar taron yaye daliban Jami’ar Calabar da ta yaye dalibai 13,610 a bikin kammala zangon karatun 2024/2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng