'Wani gwamnan Najeriya Zai Mutu Kafin 2027': Malami Ya Hango Makomar Atiku, Tinubu

'Wani gwamnan Najeriya Zai Mutu Kafin 2027': Malami Ya Hango Makomar Atiku, Tinubu

  • Fasto Ekong Ituen na Christ Deliverance Ministries ya yi hasashen cewa wani gwamna mai ci a Najeriya na iya rasa ransa sakamakon wata cuta mai sarkakiya
  • Malamin ya yi gargadi cewa Sanata Godswill Akpabio, na fuskantar barazanar rashin lafiya da kuma tsigewa daga 'yan majalisar dattawa
  • Faston ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan wani bore da zai iya haifar da matsala ga gwamnatinsa yayin da Atiku Abubakar zai hana PDP cin zaben 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Fasto Ekong Ituen na Cocin Christ Deliverance Ministries ya hango cewa wani gwamna mai ci a Najeriya zai iya rasa rayuwarsa sakamakon wata cuta mai sarkakiya.

Malamin addinin Kiristan ya bayyana cewa cutar tana da alaka da dalilai na ruhaniya da na likitanci, amma ana iya dakile hakan idan an ɗauki matakan da suka dace.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Malamin addinin Kirista ya hango makomar Atiku, Tinubu da Jonathan a 2027
Malamin addinin Kirista ya hango makomar Atiku, Tinubu da Jonathan a 2027. Hoto: @atiku, @officialABAT, @GEJonathan
Asali: Twitter

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, faston, wanda aka sani da hangen nesa, ya yi bayani kan abubuwan da za su iya faruwa a 2025 zuwa 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar Fasto Ekong Ituen:

“Shekarar 2025 za ta fi ta baya kyau. Za a samu ci gaban tattalin arziki, canjin arziki daga hannun wasu zuwa wasu, da ingantattun ayyukan gwamnati.”

Matsalar lafiya ga Akpabio da makomar Jonathan

Malamin addinin ya yi gargadin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, na fuskantar matsalar lafiya mai tsanani da ka iya hana shi gudanar da ayyukansa.

Fasto Ekong ya ce:

“Akpabio yana bukatar aukin Allah don kauce wa matsananciyar rashin lafiya. Kuma dole ne ya shirya fuskantar ‘yan adawa da ke shirin tsige shi.”

A kan batun zaɓen 2027, malamin ya shawarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da kada ya tsaya takara, yana mai cewa zai sha kaye kuma a kunyata shi.

Kara karanta wannan

Awanni da nada sababbin hadimai, Abba ya ba su umarnin bayyana yawan kadarorinsu

“Ina shawartar Jonathan da kada ya bari ya kamu da sha’awar takarar shugaban kasa a 2027, domin ba zai yi nasara ba. Zai fuskanci tozarci."

- Fasto Ekong.

Gargadi ga Tinubu da makomar Atiku a 2027

Babban faston ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da ya kula da jin daɗin magoya bayansa domin guje wa wani bore da zai iya haifar da matsala a gwamnatinsa.

“Ina ganin wani bore da ka iya yin illa ga Tinubu. Ya kamata ya kula da jin daɗin waɗanda suka yi aiki tuƙuru wajen nasararsa,” a cewar Fasto Ekong.

A kan rikicin PDP, malamin ya ce jam’iyyar na iya durƙushewa kafin 2027 idan Atiku Abubakar bai janye burinsa na takarar shugaban kasa ba.

Fasto Ekong ya ce:

“Ina shawartar shugabannin PDP da kada su ba Atiku tikitin takara. Idan ya janye, rikicin jam’iyyar zai lafa."

Hakazalika, ya yi hasashen cewa jam’iyyar APC za ta fuskanci rikicin shugabanci sakamakon sabanin ra’ayi da rashin amana kafin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Gargadi kan lafiyar wani gwamnan Najeriya

Prophet Ekong ya hango makomar wani gwamnan Najeriya kafin 2027
Prophet Ekong ya yi hasashen cewa wani gwamnan Najeriya zai mutu kafin 2027. Hoto: Prophet Ekong Ituen Ministries
Asali: Facebook

Da ya koma kan hasashen da ya yi kan wani gwamna mai ci, Fasto Ituen ya jaddada cewa sai da addu’a da shiri na musamman za a iya hana wannan masifa.

Ya ce:

“2025 shekara ce mai albarka, amma wani gwamna na iya rasuwa kafin wa’adinsa ya ƙare saboda wata gajeriyar cuta mai nasaba da ruhaniya da likitanci.”

Sai dai malamin ya bayyana cewa ana iya dakile wannan bala’i idan aka ɗauki matakan da suka dace don kare lafiyar gwamnan.

“Ina kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen yin addu’a da azumi domin samun shigar Allah a cikin lamarin,” inji shi.

A ƙarshe, Ituen ya ce duk da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, akwai alamun ci gaba a gaba, yana mai bukatar jama’a su kasance da fata mai kyau.

Malami ya hango matsalar da ke tunkaro Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamin addinin Kirista, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa ‘yan Najeriya za su fuskanci matsananciyar tsadar rayuwa a 2025.

A cewarsa, hauhawar farashin kayayyaki zai tsananta a badi, lamarin da zai kara jefa al'umma cikin kuncin rayuwa, sai dai idan an dauki matakan rage radadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.