Tafsirin Ramadan Ya Tsaya, Fitaccen Malamin Musulunci Ya Rasa Mahaifiyarsa a Borno
- An shiga jimami a Maiduguri bayan rasuwar mahaifiyar Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar wanda shi ne babban limamin masallacin Indimi
- Sanarwar rasuwar ta fito ne daga shafin Facebook na malamin, inda ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta rasu bayan fama da jinya
- Rahotanni sun ce an gudanar da sallar jana'iza ranar Asabar 22 ga Maris, 2025 a babban masallacin 505 da ke Maiduguri da misalin karfe 10:00 na safe
- Bayan sanarwa da aka fitar, majiyoyi sun tabbatar da cewa an riga an yi sallar jana’izar marigayiyar kamar yadda Musulunci ya koyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - An shiga jimami a birnin Maiduguri bayan sanar da rasuwar mahaifiyar fitaccen malamin Musulunci.
An sanar da rasuwar mahaifiyar Farfesa Muhammad Alhaji Abubakar a daren ranar Juma'a 21 ga watan Maris, 2025.

Asali: Facebook
Babban malamin Musulunci ya yi rashin mahaifiya
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin fitaccen malamin ya wallafa a manhajar Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, babban limamin masallacin Indimi ya ce ya rasa mahaifiyarsa bayan ta sha fama jinya.
Shehin malamin ya ce za a yi jana'izarta a yau Asabar 22 ga watan Maris, 2025 a masallacin 505 da ke Maiduguri a jihar Borno.
Sanarwar ta ce:
"Innalilahi wa'inna ilahi raji'un.
"Mahaifiyar Farfesa Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar babban limamin masallacin Indimi ta rasu.
"Za a yi sallar jana'izarta a gobe (Asabar) 22 ga watan Maris, 2025 wanda ya yi daidai da 22 ga watan Ramadan, 1444AH da misalin karfe 10:00 na safe a babban masallacin 505.
"Muna addu'ar Allah ya gafarta masa kura-kuranta ya kuma azurfa ta da gidan aljannar Firdausi."

Asali: Facebook
Yaushe aka gudanar da sallar jana'izar marigayiyar?
Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni aka yi sallar jana'izar marigayiyar da misalin karfe 10:00 na safe kamar yadda aka sanar.

Kara karanta wannan
Duniyar fina finan Najeriya ta yi rashi, fitacciyar jaruma ta rasu bayan mata tiyata
Daga bisani, malamin ya sake sanarwa inda yake tabbatar dakatar da karatun tafsirin Kur'ani da yake gudanarwa a masallaci.
Sanarwar ta ce za a dakatar da tafsirin a yau Asabar da kuma Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 har sai ranar Litinin za a dawo.
Sanarwar ta ce:
"Assalamu Alaikum,
"Sakamakon rashi da aka yi wa Malam.
"Babu Tafsiri yau da gobe sai jibi ranar Litinin In shaa Allahu.
"Allah ya gafartawa ( mama) da sauran mamatanmu."
Musulunci ya yi babban malami a duniya
Mun ba ku labarin cewa babban malamin Musulunci a duniya, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu yana da shekara 69 bayan fama da jinya na tsawon lokaci.
Majiyoyi sun nuna cewa Al-Huwaini ya kasance mashahurin malami a fannin Hadisi da ya karantar a kasar Masar da kuma sauran duniya baki daya lokacin da yake raye.
Rahotanni sun ce bayan sanarwar rasuwar Sheikh Al-Huwaini, malamai da dama a duniya da makarantun addini sun bayyana jimaminsu game da rashin da aka yi na babban malamin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng