Ramadan: Bayan Shiga Goman Karshe, Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Mai Muhimmanci

Ramadan: Bayan Shiga Goman Karshe, Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Mai Muhimmanci

  • Mai alfarma sarkin Musulmi ta hannun kungiyar JNI ya bukaci al'ummar musulmi su ci gaba da aikata ayyukan alheri har bayan watan Ramadan
  • Sultan ya kuma roƙi su dage da addu'ar neman Allah ya kawo sauƙin rayuwa da waraka a goman ƙarshe mai cike da rahama a wajen musulmai
  • A wata sanarwa da sakataren Jama'atu Nasril Islam ya fitar, ya tunatar da musulmi batun fitar da zakkatul Fitr kafin lokacin karamar sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ƙarƙashin jagorancin mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ta ja hankalin musulmi kan aikata ayyukan alheri.

JNI ta shawarci Musulmi da su nisanci komawa ga munanan ayyuka bayan kammala azumin watan Ramadan.

Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmi ya shawarci jama'a su kauracewa ayyuka mara kyau bayan wucewar watan Ramadan Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a wata sanarwa da sakataren JNI na ƙasa, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya fitar ranar Juna'a, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan Majalisa Kirista ya yi wa Musulmi bazata bayan bukatar babban limami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

JNI ta buƙaci musulmi su dage da addu'a

JNI ta bukaci Musulmi su ci gaba da yin addu’o’i domin samun nasarar fita daga duk wani bala’i da kuma neman sauƙi ga matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ke addabar ƙasa.

Sanarwar ta kuma bukaci Musulmi da su ci gaba da bayar da taimako ga fakirai, marasa galihu, marayu da naƙasassu, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki.

Sarkin musulmi ya fitar da sanarwa

"Mu na ƙara kira da tunatarwa ga Musulmin Najeriya da su su yi amfani da ranakun ƙarshe na Ramadan wajen karanta Alƙur’ani mai girma fiye da yadda aka saba.
"Mutane su ƙara dagewa da karatun Aƙkur'ani tare da fahimtar ma'anarsa kuma su yi amfani da umarni kana su guje wa abin da Allah ya hana, su ci gaba da ayyukan ibada bayan watan Ramadan."

- In ji JNI.

Haka kuma JNI ta tunatar da Musulmi wajibcin bayar da Zakatul-Fitr, wanda ake bayarwa a kwanaki uku na ƙarshe na Ramadan ko kuma da safiya kafin Sallar Eid-el-Fitr.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Babban jigo a APC ya gana da Atiku, ya fadi shirin kifar da Tinubu

JNI ta yi wa musulmai fata na gari

Daga karshe JNI karkashin sarkin Musulmi ta yi fatan Allah ya gafartawa musulmk baki ɗaya kuma Ya karɓi ibadunsu.

"Mu na yi wa Musulmi fatan samun gafarar Allah a cikin waɗannan ranaku masu daraja da bayan su, tare da addu’ar Allah ya karɓi ibadunmu.
"Haka nan, mu na jaddada bukatar cewa Musulmi su guji komawa ga ayyukan da suka sabawa koyarwar addini bayan kammala azumin Ramadan."

JNI ta kuma bukaci al’umma da su kasance masu riko da kyawawan halaye da suka koya a cikin watan Ramadan, tare da ci gaba da bin hanyoyin da za su kyautata zamantakewa da kawo ci gaba mai ɗorewa.

Wani malami, Malam Yahuza ya ce ana son mutum ya ci gaba da ayyukan alheri, ya gujewa aikata saɓo ko da bayan watan azumin Ramadan.

Da yake ƙarin haske kan jan hankalin da sarkin Musulmi ya yi yayin hira da wakilin Legit Hausa, ya ce azumi wata ne da ake son mutane su gyara halayensu.

Kara karanta wannan

Zo ka nema: Gwamna Fintiri zai horar da matasa, akwai tukuicin N10,000 duk wata

Malam Yahuza ya ce:

"Ba iya watan ake so musulmi ya gyara halayensa ba, a kowane lokaci Allah yana son mutane su tuba su daina aikata saɓo."
"Saboda haka yana da kyau musulmai su ɗore a kan kyawawan ayyukan da suka yi a Ramdan, taimakon marasa karfi, sadaƙa, karatun Alƙur'ani da sauransu."
"Idan muka gyara halayenmu, babu ko shakka Allah zai magance mana abubuwan da ke damunmu, kamar matsalar tsaro, yunwa da sauransu, Allah karɓi ibadunmu."

Alamun gane Lailatul Qadr a Ramadan

A wani labarin, mun tattaro maku manyan alamun da ake gane daren Lailatul Qadr a goman karshe na azumin watan Ranadan.

Wannan dare ya fi watanni 1,000 daraja kamar yadda Allah S.W.T ya bayyana a cikin Alƙur'ani mai girma, sura ta 97, aya ta uku (Suratul Al-Qadr 97:3).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng