'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Abuja, Sun Yi Awon Gaba da Babbar Soja da Wasu Mutane

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Abuja, Sun Yi Awon Gaba da Babbar Soja da Wasu Mutane

  • Wasu tsagerun ƴan bindiga sun kai hari a babban birnin tarayya a daren ranar Juma'a, 21 ga watan Maris 2025
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da wata babbar jami'ar sojin ruwa tare da wasu mutane a yankin Mpape na birnin Abuja
  • Jami'an tsaro sun bazama domin ganin sun kuɓutar da mutanen tare da cafke ƴan bindigan da suka yi garkuwa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan sun sace wata jami'ar sojin ruwan Najeriya da wasu mutum biyu a yankin Mamman Vatsa da ke kan hanyar Mpape a birnin Abuja.

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja
'Yan bindiga sun sace babbar soja a Abuja Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Kaduna: Miyagu sun farmaki masallaci ana tsaka da Sallah, an samu asarar rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Maris, 2025, da misalin karfe 7:45 na dare, lokacin da ƴan bindigan suka buɗe wuta tare da sace mutanen.

Ƴan bindiga sun kai hari a Abuja

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigan guda hudu, waɗanda ke ɗauke da makamai, sun yi harbi ba kakkautawa sannan suka yi awon gaba da mutane uku.

An bayyana sunayen mutanen a matsayin, Laftanar Cynthia Ako, jami’ar sojin ruwa ta Najeriya, Gold Alfred, mazaunin yankin Bwari da kuma wani mutum ɗaya da har yanzu ba a tantance sunansa ba.

Majiyoyin sun ƙara da cewa mutanen da aka sace su na kan hanyarsu ta komawa gida a cikin motarsu ne bayan sun kai ziyara ga wani ɗan uwansu mai suna Blessing Akor a Beggar Quarry, Mpape.

Sun ƙara da cewa Laftanar Cynthia Ako tana aiki ne da hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe jami'an sojoji a wani kazamin farmaki da suka kai Benuwai

Jaridar The Punch ta rahoto cewa ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N100m kafin su sako mutanen.

Jami'an tsaro sun fara bincike

Bayan aukuwar wannan lamari, rundunar sojojin Najeriya da sashen yaƙi da garkuwa da mutane na hukumar ƴan sanda ta babban birnin tarayya Abuja sun fara bincike kan lamarin.

Sun fara binciken ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin sa-kai da kuma mafarauta na yankin, domin gano inda aka kai mutanen da kuma cafke ƴan bindigan.

Har ila yau, jami’an tsaro sun bazama a dazuka da wuraren da ake zargin masu garkuwa da mutane ke fakewa a yankunan da ke kewaye da Mpape domin ceto mutanen da aka sace.

Wannan sabon hari ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin Mpape da kewaye, suka buƙaci hukumomi su ɗauki matakan gaggawa don magance matsalar garkuwa da mutane da ke ƙaruwa a Abuja.

Ƴan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun tafka ta'asa bayan sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun hallaka Muhammad Adamu wanda ke shugabantar Miyetti Allah a ƙaramar hukumar Barikin Ladi, bayan sun kai masa hari har cikin gidansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng