Pantami Ya Magantu bayan Aminu Ado da Sanusi II Sun Sanar da Lokutan Idi a Kano

Pantami Ya Magantu bayan Aminu Ado da Sanusi II Sun Sanar da Lokutan Idi a Kano

  • Isa Ali Pantami ya nuna damuwa kan rikicin sarautar Kano da ake tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II
  • Malamin musuluncin ya ce ba a taba tunanin za a ga haka a Kano ba, ya bukaci mutane su rika hakuri don samar da mafita
  • Sheikh Pantami ya kuma koka kan yadda tarbiyya da tattalin arziki suka tabarbare a Arewa, yana mai kira da a nemi mafita

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana damuwarsa kan halin da Arewa ke ciki, musamman rikicin sarautar Kano da matsalar tarbiyya da tattalin arziki.

Malamin ya bayyana hakan ne a yayin tafsirin Ramadan da ya gabatar a rana ta 21 a birnin tarayya Abuja, inda ya ce dole ne Arewa ta tashi tsaye domin magance matsalolinta.

Kara karanta wannan

'Ayi hankali': Abin da shugaban rikon kwarya ya fada bayan shiga ofis a Rivers

Sheikh Pantami
Sheikh Pantami ya yi magana kan rikicin siyasar Kano. Hoto: Professor Isa Ali Pantami|Masarautar Kano
Asali: Facebook

A bidiyon da aka wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Pantami ya bukaci jama’a da su rika hakuri tare da saka bukatun al’umma a gaba don samar da mafita mai dorewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isa Pantami ya magantu kan rikicin Kano

A tafsirin da ya gabatar, Sheikh Pantami ya nuna damuwa kan rikicin sarauta da ake fama da shi a Kano. Ya ce yana da matukar tayar da hankali a samu iyayen kasa har biyu a jiha daya.

Malamin ya ce Kano jiha ce mai matukar muhimmanci ga Arewa, don haka akwai bukatar a magance rikicin.

Ya bukaci mutane su daina sanya bukatun kansu a gaba, su nemi mafita da za ta amfani al'umma gaba daya.

Sanusi
Aminu Ado da Sanusi II. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Twitter

A makon da ya wuce gwamnan jihar Kano ya sanar da cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II zai yi hawan sallah bayan sallar idi.

Kara karanta wannan

Yadda Sheikh Pantami ya kubuta daga sharrin 'yan fashi bayan harbi 3 a titi

Haka zalika, Musa Iliyasu Kwankwaso ya sanar da cewa mai martaba Aminu Ado Bayero ma zai yi sallar idi a jihar.

Sheikh Pantami ya yi addu'ar zaman lafiya

Sheikh Pantami ya yi doguwar addu’a yana rokon Allah ya kawo karshen rikicin Kano. Ya kuma roki Allah da ya kare Kano daga kowanne irin tashin hankali da zai iya tasowa.

Baya ga haka, malamin ya roki Allah ya kare dukkan jihohin Arewa daga irin rikicin sarautar da ke faruwa a jihar Kano.

Maganar rashin tarbiyya a Arewa

Sheikh Pantami ya bayyana damuwa kan yadda tarbiyya ta lalace a Arewa, ya ce a baya ana girmama manya har da masu kananan ayyuka kamar mai gadi da mai ruwa.

Haka zalika, ya ce matasa da dama sun rasa shugabanni masu shiryar da su kan harkokin rayuwa da addini.

Matsalar tattalin arziki a Najeriya

Malamin musuluncin ya koka kan yadda tattalin arziki ke tabarbarewa a Arewa.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Ya ce a baya akwai manyan kamfanoni da ake da su a Kano, Funtua, Zariya da sauransu, amma yanzu yawancinsu sun mutu.

Sheikh Pantami ya ce abin takaici ne a ce Arewa ba ta iya kera kayayyakin yau da kullum da ake amfani da su.

Ya ce kamata ya yi Arewa ta habaka harkokin masana’antu fiye da hada kamfanonin shinkafa da ruwan leda kacokam.

Haduwar Sheikh Pantami da 'yan fashi

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya ba da labarin yadda ya hadu da 'yan fashi a kan hanyar Gombe zuwa Borno.

Malamin ya ce wata rana a kusa da Damboa, 'yan fashi suka tare su kuma har aka masa harbi uku amma Allah ya sa rayuwarsa na gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng