Dattawan Arewa Sun Faɗi Damuwarsu kan Dokar Ta Ɓaci a Ribas, Sun Ambaci Kano
- Dattawan Arewa sun buƙaci Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta maida Gwamna Simi Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisa kan kujerunsu
- Mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa (NEF), Abubakar Jika Jiddere ya ce babu dalilin ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Ribas
- NEF ta kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hana rikicin siyasa yaɗuwa zuwa wasu jihohi kamar Kano a Arewacin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta nuna rashin jin daɗinta kan rikicin siyasa da ya faru a jihar Rivers, wanda ya kai ga dakatar da Gwamna Simi Fubara.
Ƙungiyar NEF ta yi watsi da matakin shugaban ƙasa, Bola Ahked Tinubu ya ɗauka na dakatar da gwamna, mataimakiyarsa da ƴan Majalisar Dokokin Ribas.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin NEF, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya fitar kan halin da ake ciki a jihar Ribas, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
Wike ya sake samun nasara, Kotun Koli ta yi hukunci kan rikicin sakataren PDP na ƙasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NEF ta bukaci Tinubu ya dawo da Fubara
Ƙungiyar dattawan Arewa ta bukaci Shugaban Ƙasa da ya gaggauta mayar da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa kan kujerarsu.
NEF ta lura cewa duk da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya ba wa shugaban ƙasa ikon ayyana dokar ta-baci a kowace jiha idan ta kama, babu dalilin ɗaukar matakin a Ribas.
"Shugaban ƙasa na da ikon ayyana dokar ta-baci a kowace jiha ko yanki na ƙasa ta hanyar wallafa sanarwa.
"Amma duk da haka shugaban ƙasa ba zai ɗauki wannan mataki ba dole sai idan ɗaya daga cikin sharuɗɗan da ke cikin sashe na 305, sakin layi na 3 ya faru."
Sharuddan kafa dokar ta ɓaci a Najeriya
Sharuɗɗan da aka lissafa a sashe na 305 (3) sun haɗa da:
- Yakin basasa ko mamaya daga ƙasashen waje
- Rushewar doka da oda
- Barazanar kai hare-hare
- Bala'i ko annoba
- Wani yanayi da ke barazana ga lafiyar jama’a.

Kara karanta wannan
Tinubu ya jawo wa kansa, dattawan Ribas sun faɗi matsayarsu kan dakatar da gwamna
"Kowa ya san babu wani daga cikin waɗannan sharuɗɗan da ya faru a jihar Rivers. Sai dai idan akwai wata manakisa da ministan Abuja, Nyeson Wike ya shirya saboda son zuciya, ba don alfanun jama'a ba
- In ji Dattawan Arewa.
Kungiyar NEF ta yi kira ga gwamnatin tarayya da shugaban ƙasa da su nemo mafita mai dorewa ga rikicin siyasar jihar Ribas.

Asali: Facebook
Dattawan Arewa sun yi gargaɗi kan Kano
Dattawan sun bukaci a gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa gwamnan, mataimakinsa da kuma ’yan Majalisar Dokoki na jihar, domin dawo da adalci da bin doka.
NEF ta gargadi Gwamnatin Tarayya da kada ta bari rikicin siyasa ya yaɗu zuwa wasu jihohin kamar Kano, inda a halin yanzu ake fama da rikici kan sarautar Kano, The Cable ta rahoto.
An ba kowane sanata $15,000?
A wani labarin, kun ji cewa Godswill Akpabio ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa ya ba kowane sanata $15,000 don su goyi bayan ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.
Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana cewa rahoton da ake yaɗawa ƙarya ne, wasu ne suka kirkiro labarin domin ɓata masa suna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng