Yadda Gwamnoni Ke Matsawa Tinubu kan Ƴancin Kananan Hukumomi, an Gano Shirinsu
- Gwamnoni na ƙoƙarin hana aiwatar da hukuncin da ke bai wa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kai da kudinsu kai tsaye
- A ganawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu, gwamnoni sun nuna rashin amincewa da a tura kuɗi kai tsaye zuwa asusu ta CBN
- Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnoni sun nemi a rika tura kuɗi zuwa bankunan kasuwanci, ba bankin CBN da ke karkashin hukuma ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Gwamnatocin jihohi suna matsin lamba ga shugaba Bola Tinubu domin hana tabbatar da hukuncin kotun koli kan ‘yancin kananan hukumomi da kuɗinsu kai tsaye.
A wani taro a fadar shugaban kasa, wasu gwamnoni sun nemi a dakatar da tsarin har sai an biya basussukan da ake bin kananan hukumomi.

Asali: Twitter
Kotu ta raba gardamar kudin kananan hukumomi
Wani jami’in fadar shugaban kasa ya ce taron bude-baki ya zama dama ga gwamnoni domin tattaunawa da shugaban kasa kan batun kudin, cewar Leadership Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 11 ga Yuli, kotun koli ta yanke hukuncin cewa ya zama dole a rika biyan kuɗin kananan hukumomi kai tsaye.
Kotun ta tabbatar da cewa tsarin yana da tushe a cikin kundin tsarin mulki na 1999 da ke kare 'yancin hukumomi.
Alkalai sun ce ba daidai ba ne gwamnoni su ci gaba da rike kuɗin kananan hukumomi ko nada shugabanni ba tare da zabe ba.
Ta kuma bayyana cewa sai an zabi shugabannin kananan hukumomi ne kawai za su samu kuɗin kai tsaye daga asusun tarayya.
Gwamnoni sun matsa kan yancin kananan hukumomi
A cewar wata majiya, gwamnoni sun gana da shugaban kasa a ranar Talata domin neman mafita kan batun bai wa kananan hukumomi 'yanci.
Wata majiya ta ce:
"Gwamnoni sun gana da shugaban a ranar Talata don samun mafita, suna ci gaba da kamun kafa.”
Majiyar ta ce gwamnati na so a tura kuɗi kai tsaye zuwa CBN, kuma a buɗe asusun kowane karamar hukuma a Babban Banki na Najeriya.
Amma a cewarta:
"Gwamnoni ba sa son hakan, sun ce hakan yana nufin gwamnatin tarayya ce ke da cikakken iko.”

Asali: Twitter
Bukatar gwamnoni kan kudin kananan hukumomi
Majiyar ta ce gwamnoni na so a rika turawa kananan hukumomi kuɗi kai tsaye zuwa bankunan kasuwanci ba CBN ba.
Gwamnoni sun nuna fargaba cewa idan CBN ke rike da kuɗi, ana buƙatar amincewar akanta janar na ƙasa kafin su fitar da su.
Majiyar ta ce ana ci gaba da tattaunawa domin warware matsalar, amma abin da ke faruwa shi ne kuɗaɗen na nan a tsare, cewar rahoton Punch.
CBN ya bukaci kananan hukumomi su gabatar da bayanan asusunsu na shekaru biyu domin fara biyan kuɗinsu.
A halin yanzu, CBN ya soma bude asusun banki na kananan hukumomi domin su rika karbar hakkokinsu kai tsaye.
Gwamnatin Tinubu za ta biya kananan hukumomi
Kun ji cewa kungiyar kananan hukumomin Najeriya ta bayyana cewa akwai dalilan da suka jawo har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara biyansu kudinsu ba.
Shugaban kwamitin amintattu na ALGON, Hon. Odunayo Alegbere ya ce gwamnati ta ba su hanyar saukaka masu samun kasafinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng