Kotu Ta Ceto Sanata Natasha daga Barazanar Raba Ta da Kujerarta

Kotu Ta Ceto Sanata Natasha daga Barazanar Raba Ta da Kujerarta

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta bayar da umarnin wucin gadi da ke hana INEC karbar bukatar tsige Natasha Akpoti Uduaghan
  • Ana zargin wani abokin siyasar Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ke daukar nauyin yunkurin raba Natasha da kujerarta
  • Hukuncin kotun ya biyo bayan wata buƙatar gaggawa da aka shigar a gabanta wanda ya samu wakilcin lauya Smart Nwachimere

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Lokoja, jihar Kogi, ta bayar da umarnin wucin gadi da ke hana hukumar INEC ko ma’aikatanta ko wakilanta daga karbar yunkurin tsige Sanata Natasha Akpoti.

Umarnin kotun ya kuma hana INEC gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a bisa kokarin yi wa Sanata mai Wakiltar Kogi ta Tsakiya kiranye.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Natasha
Kotu ta dakatar da yi wa Natasha kiranye Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa, umarnin ya biyo bayan wata buƙatar gaggawa da Anebe Jacob Ogirima da wasu mutum hudu suka shigar a gaban kotu don neman umarnin wucin gadi na hana yi wa Sanatar kiranye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta dakatar da INEC kan Natasha

Daily post ta ruwaito cewa mutanen sun samu wakilcin lauya Smart Nwachimere, Esq., daga ofishin West-Idahosa, SAN & Co., kuma kotun ta amince da bukatarsu ranar Alhamis.

A hukuncin da mai shari’a Isa H. Dashen ya yanke a cikin shari’a mai lamba FHC/LKJ/CS/13/2025, ya bayyana cewa:

“Bisa wannan bukata ta wucin gadi da aka shigar a ranar 19 ga Maris, 2025, sannan aka yi wa rajistar wannan babbar kotu a ranar 20 ga Maris, 2025, ana roƙon kotu da ta bayar da umarni kamar haka:"
"Kotun ta bayar da umarnin wucin gadi da ke hana INEC gudanar da kuri’ar jin ra’ayi bisa irin wannan ƙorafi har sai an yanke hukunci kan takardar da aka shigar a gaban kotu.”

Kara karanta wannan

Wike ya sake samun nasara, Kotun Koli ta yi hukunci kan rikicin sakataren PDP na ƙasa

Kotun ta sanya ranar sauraron ƙarar Natasha

Kotun ta bayyana cewa za ta ci gaba da sauraron karar a ranar 6 ga Mayu, 2025, domin bayar da rahoto kan isar da takardun shari’a da kuma ƙarin bayani.

Natasha
Kotu ta sa ranar ci gaba da sauraron ƙara kan Natasha Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Twitter

A farkon makon nan, an samu rahotannin cewa ana shirin gudanar da tsarin kiranye, wanda ake zargin wani abokin siyasar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ke daukar nauyinsa.

Natasha ta zargi Akpabio da taba jikinta

A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da yin maganganun cin zarafin mata a kanta.

Zargin na Natasha ya zo ne yayin da ake cigaba da takaddama kan dakatar da ita da aka yi, wanda yanzu haka take shari’a a kotu da bukatar da wasu ke yi na a tsige Sanatar.

Ta bayyana cewa Godswill Akpabio na yawan yi mata kalamai masu cin mutunci a lokuta daban-daban, har ma a gaban wasu sanatoci hade da yi mata kallon cin zarafi idan ya samu dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel