ALGON: "Gwamnatin Tarayya Ta Sa Sharadin Biyan Kananan Hukumomi Kudi Kai Tsaye"
- Kungiyar kananan hukumomin Najeriya ta bayyana cewa akwai dalilan da suka jawo har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara biyansu kudinsu ba
- A shekarar da ta gabata ne kotun kolin kasar nan ta tabbatar wa da kananan hukumomi 'yancin gashin kansu, har da umarnin a ba su kasonsu
- Hon. Odunayo Alegbere, wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na ALGON ya ce gwamnati ta ba su hanyar saukaka masu samun kasafinsu
- Sannan ya caccaki tsarin yadda ake gudanar da zaben kananan hukumomi, wanda ya ce yanzu haka ana kokarin gyara doka kan batun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara rabon kudi kai tsaye ga kananan hukumomi ba saboda ana ci gaba da aiwatar da wasu tsare-tsare masu muhimmanci.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON), Hon. Odunayo Alegbere, ne ya tabbatar da hakan.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito Alegbere ya bayyana cewa an umarci kananan hukumomi da su bude asusu a Babban Bankin Najeriya (CBN) domin saukaka aiwatar da rabon kudaden kai tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yaba wa gwamnatin tarayya kan kokarinta, musamman bisa hukuncin kotun koli da ke tabbatar da ‘yanci da cin gashin kan kananan hukumomi a bangaren kudi.
ALGON ta fadi amfanin biyansu kudinsu
Hon. Odunayo Alegbere ya tabbatar da cewa rabon kudi kai tsaye zai taimaka wajen rage talauci ta hanyar ba kananan hukumomi damar amfani da kudaden su yadda ya dace.
Ya amince cewa har yanzu ba a kammala shirin ba su cikakken ‘yancin cin gashin kai ba, amma yana ganin an fara samun ci gaba a hankali.

Asali: Getty Images
Hon. Alegbere ya kara da cewa ba matakin zai bunkasa ayyukan kananan hukumomi daga tushe, wanda ake sa ran zai taimaka wajen kara yalwar arziki tsakanin jama'a.
ALGON ta soki tsarin zaben kananan hukumomi
Shugaban kwamitin amintattu na ALGON ya soki yadda gwamnatocin jihohi ke gudanar da zabukan kananan hukumomi.
Ya ce galibi hakan ya na haifar da nadin shugabanni maimakon zaben gaskiya da ba jama'a zaben wanda suke so.
Sai dai ya tabbatar da cewa ana kan gyaran kundin tsarin mulki a majalisar dokoki ta kasa, wanda zai kawo mafita a wannan lamari.
Ya ce:
“Mun yi farin ciki da shugaban kasa, kuma ko da yake ba mu kai ga burinmu ba tukuna, amma muna samun ci gaba a hankali.
ALGON ta dauki matsaya kan albashi
A baya, mun wallafa cewa kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) ta bayyana cewa zai yi wahala ga kananan hukumomi a Najeriya su iya biyan ma’aikata sabon mafi karancin albashi.
Shugaban ALGON na kasa, Aminu Muazu-Maifata, ya bayyana cewa biyan mafi karancin albashi abu ne mai wahala sosai ga kananan hukumomi duba da yanayin samunsu da wasu dalilan.
Ya ce bisa la'akari da kason da ake samu daga asusun FAAC, babu wata karamar hukuma a Najeriya da za ta iya biyan N62,000, balle kuma ayi maganar biyan N250,000.
Asali: Legit.ng