ALGON ta tsige mataimakin shugaban ta na ƙasa, Soba, ta maye gurbinsa da wani

ALGON ta tsige mataimakin shugaban ta na ƙasa, Soba, ta maye gurbinsa da wani

- Kungiyar shugabannin ƙananan hukumomi, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa, Aliyu Soba an maye gurbinsa da Jega Shehu

- Kakakin kungiyar, Obiora Orji ya sanar da cewa an tsige ne saboda ya karya wasu dokokin da kungiyar

- A bangarensa, Soba ya ce ba a sanar da shi batun tsige shi ba kuma ba a bashi dama ya kare kansa ba idan ana tuhumar da wani abu

Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.

Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar.

ALGON ta tsige mataimakin shugaban ta na ƙasa, Soba, ta maye gurbinsa da wani
Mohammed Aliyu Soba. Hoto @dailynigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno

Sanarwar da Kakakin ALGON, Obiora Orji ya bawa kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Laraba a Abuja ya nuna ƙungiyar ta zaɓi Jega Shehu ya maye gurbin Soba.

Orji ya ce dukkan ƴan Majalisar Zartarwa na Ƙungiyar da Kwamitin Amintattu sun amince da tsige Soba a taron da suka yi a ranar Laraba a Asaba, jihar Delta.

Ya ce an tsige Soba ne saboda saɓa wasu dokoki na kundin tsarin kungiyar ta ALGON.

A bangarensa, Soba ya ce bai da masaniya kan batun tsige shi yayin hirar wayar tarho da ya yi da wakilin NAN.

KU KARANTA: Dalilin da yasa 'yan daba suka tube wa Fayose hula a Ondo

Ya bayyana tsigewar da aka ce an masa a matsayin abin zargin don ba su da ikon tsige shi.

"Zaɓe na aka yi don haka idan za a tsige ni sai a bi dokokin da ke kundin tsarin mulkin jam'iyya.

"Idan har za a kira taron NEC a tsige ni tabbas akwai dalili kuma ban san dalilin ba.

"Kafin a tsige ni, ya dace a bani damar kare kaina kan zargin da ake min.

"Idan akwai wani zargi da aka yi wa ofishi na, kamata ya yi su sanar da ni sai in kare kai na," a cewar Soba.

Mista Soba ya ƙara da cewa idan an sanar da shi cewa an tsige shi a hukumance, zai sanar da matsayin sa da na kungiyar reshen jihar sa.

A wani labarin daban, Shugaba Buhari ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ke neman yi.

Gwamnan da aka zaɓa a karon farko a 2017 yana fatar zarce wa kan mulki idan al'ummar jihar sun dake zabensa a zaɓen da za ayi ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel