Awanni da Nada Sababbin Hadimai, Abba Ya Ba Su Umarnin Bayyana Yawan Kadarorinsu
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci hadimansa da su bayyana kadarorinsu ga Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB)
- Gwamna Abba ya ce wannan mataki zai taimaka wajen kauce wa tuhumar su da karya dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya
- Haka kuma, ya karrama wasu daga cikin shugabannin hukumomi 13 bisa goyon bayansu ga gwamnati da jajircewarsu wajen aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkannin hadiman siyasa da ya nada da su bayyana kadarorinsu a gaban hukumar da'ar ma’aikata ta kasa.
Ya bayanar da umarnin ne a ranar Alhamis, tare da bayyana cewa bayyana yawan kadarorin zai taimaka wajen dakile duk wata matsala da za ta iya taso wa a nan gaba.

Asali: Facebook
Wannan umarni na kunshe cikin wata sanarwa da Darekta Janar kan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya yi bude baki da hadimansa
Gwamna Abba ya ba da umarnin ne yayin liyafar bude baki da ya shirya tare da shugabannin hukumomin gwamnati da mashawartansa na musamman a fadar gwamnatin Kano.
Sanarwar da Sunusi Bature Dawakin Tofa ta fitar ta ce:
“Hukumar da'ar ma’aikata ta Kano ta sanar da ni cewa 60% zuwa 70% na hadiman siyasa na jihar ba su yi rajista da su ba.
“Sun roke ni da in umarce ku da ku cika takardun bayyana kadarori don gujewa matsalolin rashin bin dokar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.”
Gwamnan Abba ya shawarci mashawartansa
A yayin taron, gwamnan ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu mashawarta na musamman suka gaza shawartar gwamnati da bak ko a rubuce.
Ya ce:
“Ya fi dacewa mashawarta su aiko min da takardu da dama a kan a shafe fiye da shekara guda ba a bayar da wata shawara a kan harkokin mulki ba.”

Asali: Facebook
Ya bukace su da su gyara wannan hali ta hanyar sanya ido kan al’amuran da suka shafi ofisoshinsu tare da mikawa gwamnati rahotanni, ko da kuwa korafe-korafe ne.
Abba ya rabawa shugabannin hukumomi kujerun hajji
Gwamna Yusuf ya jinjinawa shugabannin hukumomi bisa goyon bayansu ga gwamnatinsa, tare da yaba wa da kokarinsu ta hanyar ba su kyautar kujerun aikin hajji ga mutum 13.
Da take magana a madadin shugabannin hukumomi, Shugabar hukumar adashin gata na lafiya ta Kano (KCHIMA), Dakta Rahila Mukhtar, ta gode wa gwamnan bisa tallafinsa.
Ta kuma bukace shi da ya ci gaba da yi musu gyara idan sun yi kuskure don daidaita su da manufofin gwamnatinsa.
Ana fargabar barazana ga gwamnatin Abba

Kara karanta wannan
Tsohon hadimin Jonathan ya dauko zancen tsige Tinubu kan dakatar da Gwamnan Ribas
A baya, kun ji cewa fitacciyar 'yar siyasa a Arewacin Najeriya, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta nuna damuwa kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da mulkin kasar nan.
Ta bayyana fargabar gwamnati za ta iya amfani da barazana da dokar ta-baci domin cimma burinta a siyasa ta hanyar dakile manyan jihohin, musamman Kano, kafin zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng