Jira Ya Kare: Shugaban NYSC Ya Fadi Lokacin Fara Biyan Alawus na N77,000

Jira Ya Kare: Shugaban NYSC Ya Fadi Lokacin Fara Biyan Alawus na N77,000

  • Shugaban hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ya faranta ran matasa
  • Ya bayyana cewa daga watan Maris na 2025 za a fara biyan matasa masu yi wa ƙasa hidima alawus na N77,000 duk wata
  • Shugaban na NYSC ya buƙace su da su ci gaba da jajircewa da sadaukarwa wajen hidimtawa ƙasa lokacin da ake kuka tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya bayyana lokacin fara biyan alawus na N77,000.

Shugaban na hukumar NYSC ya bayyana cewa dukkan matasan da ke yi wa ƙasa hidima za su karɓi sabon alawus ɗin su na N77,000 daga watan Maris, 2025.

NYSC za ta fara biyan alawus na N77,000
Shugaban NYSC ya ce za a fara biyan N77,000 a watan Maris Hoto: National Youth Service Corps
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da hukumar NYSC ta sanya a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, 20 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Rivers: An shiga fargabar halin da Fubara ya shiga kwanaki 2 bayan dakatar da shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NYSC na son jin daɗin masu yi wa ƙasa hidima

Ya ce hukumar NYSC da gwamnatin tarayya suna da alhakin kula da jin daɗin matasan, kuma za su ci gaba da ba da fifiko kan walwalarsu a kowane lokaci.

Darakta-Janar na NYSC ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, yayin da yake tattaunawa da matasan da ke yi wa ƙasa hidima a ofisoshin NYSC na yankunan Wuse da Garki a babban birnin tarayya, Abuja.

Ya ce hukumar NYSC da gwamnatin tarayya suna da alhakin kula da jin daɗin matasan, kuma za su ci gaba da ba da fifiko kan walwalarsu a kowane lokaci.

Birgediya Janar Nafiu, wanda ya yi godiya ga matasan saboda sadaukarwar da suke yi wa ƙasa, ya shawarce su da su kasance masu hankali, jajircewa da ɗa’a yayin da suke hidimtawa ƙasar nan.

Ya yabawa waɗanda suka kafa shirin NYSC bisa hangen nesa da suka yi wajen ƙirƙiro shi, tare da yin kira ga kowa da kowa da ya marawa shirin baya.

Kara karanta wannan

Rigima ta ɓarke a jihar Kano da FAAN ta fara rusa gidajen mutane a watan azumi

Birgediya Janar Nafiu ya ƙara da cewa shirin NYSC babbar dama ce da ke samar haɗin kai da sada zumunci, ta yadda matasa masu digiri ke koyon al’adu da darussan rayuwa a wuraren da ba a haife su ba.

NYSC za ta koyawa matasa ɗabi'un kirki

Ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da koyawa matasa ɗab'iu irin su kishin ƙasa, ɗa’a, biyayya, halayen kirki, basirar jagoranci da aiki tare da juna.

"Daga watan Maris, za ku fara karɓar N77,000 a matsayin alawus na wata-wata. NYSC na da cikakken tsari na adana bayanai, kuma ina tabbatar muku cewa za a biya ku haƙƙokin ku."
"Ƙasar nan da hukumar NYSC suna jin daɗin hidimar da kuke yi."

- Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu

A madadin takwarorinta a yankin Garki, wata matashiya mai hidimtawa ƙasa, Zaka Deborah Alheri (FC/24A/5831), ta jinjinawa shugaban bisa ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da an biya su sabon alawus ɗin su.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya naɗa sababbin mukamai, tsohon mai adawa da gwamnati ya rabauta

Hukumar NYSC ta samu sabon shugaba

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon shugaba ga hukumar kula da masu yi wa hidima (NYSC).

Shugaban ƙasan ya naɗa Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu a matsayin wanda zai maye gurbin Birgediya Janar Yusha'u Ahmed a shugabancin hukumar NYSC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng