Dubu Ta Cika: Sojoji na tsaka da Farautar Bello Turji, an Cafke Hatsabiban Ƴan Bindiga 2
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wasu kasurguman ƴan bindiga biyu da dillalin makamai a jihohin Zamfara da Sakkwato
- Mai magana da yawun rundunar tsaro na kasa, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana hakan a taron manema labarai ranar Alhamis
- Ya ce sojojin sun samu nasarori da dama a yaƙi da ƴan tada ƙayar baya a makon da ya shige daga ranar 15 zuwa 20 ga watan Maris, 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yayin da rundunar sojojin Najeriya ke ci gaba da farautar manyan gasurguman ƴan ta'adda irunsu Bello Turji, an samu nasara a jihohin Sokoto da Zamfara.
Dakarun Sojojin Najeriya sun cafke wasu hatsabiban ƴan bindiga guda biyu da dillalin makamai, Shehu Bagiwaye a kananan hukumomin Gudu (Jihar Sokoto) da Gusau (Jihar Zamfara).

Asali: Twitter
Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar tsaro (DHQ), Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Alhamis, Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na ɗaya daga cikin nasarorin da dakarun sojin ke ci gaba da samu a yaƙi da ƴan fashin daji da suka addabi jama'a musamman a Arewa maso Yamma.
Sojoji sun miƙa tubabbu ga gwamnati
Bugu da ƙari, kakakin Hedikwatar, Kangye ya ce rundunar ta mika tsofaffin ‘yan ta’adda guda 75 da suka miƙa wuya ga gwamnatin jihar Borno bayan an kammala canza masu tunani.
A cewarsa, daga cikin tubabbun ƴan ta'addan da aka miƙa wa gwamnatin Borno bayan horar da akwai maza bakwai, mata 34 da yara 34.
Ɓarayin mai sun shiga hannu a Najeriya
Ya ci gaba da cewa cikin makon da ya gabata (15-20 ga watan Maris, 2025), sojojin sun kama mutum 23 da ake zargi da satar man fetur tare da kwato kayayyakin da kudinsu ya kai Naira biliyan 461.7.
Manjo Janar Kangye ya ce sojojin sun gano da kuma lalata rijiyoyin haƙo mai na haram guda 42, tankunan ajiya 33, kwale-kwale 28, da haramtattun matatun mai 21.
Haka zalika a cewarsa, dakarun ba su tsaya iya nan ba, sun lalata manyan tukwane da ake sarrafa danyen mai ba bisa ƙa'ida ba guda 36.

Asali: Facebook
Makaman da aka ƙwato daga miyagu
Ya ƙara da cewa dakarun sun kwato bindigogi daban-daban ciki har da AK-47, bindigogin da aka ƙera gida, da makamai kamar gurneti (RPG) da sauransu.
Sojojin sun kuma ƙwato harsasai da dama masu nau'in 7.62mm da kuma gurneti masu fashewa watau bama-bamai duk daga hannun ƴan tada ƙayar baya.
Sauran abubuwan da aka kama sun hada da babura, kekunan hawa, wayoyin hannu, da kuma wasu motocin da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata miyagun laifuffuka.
Sojoji sun dakile shirin kungiyar ISWAP
A wani labarin, kun ji cewa dakarun haɗin guiwa na rundunar Operation Haɗin Kai sun yi nasara fatattakar mayakan ISWAP da suka yi yunkurin kai hari a Borno.
An ruwaito cewa dakarun sojojin sun fuskanci ƴan ta’addan inda suka yi musayar wuta, lamarin da ya tilasta wa maharan janyewa.
Asali: Legit.ng