Kano: Ana Fargabar Gwamnatin Tinubu za Ta Iya Watsa Dokar Ta Bacin Ribas a Jihohi
- Naja’atu Muhammad ta bayyana damuwa cewa Bola Tinubu na amfani da dokar ta-baci domin dakile zababbun shugabannin jihohi
- Ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya na kokarin mamaye wasu jihohi don bai wa Tinubu damar ci gaba da mulki bayan wa'adin farko
- Naja'atu na ganin bayan jihar Ribas, gwamnatin Bola Tinubu na hararar Kano da wasu jihohin da ta ke bukata don nasara a zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Fitacciyar 'yar gwagwarmaya a siyasar Arewacin Najeriya, Hajiya Naja'atu Muhammad, ta bayyana fargabar cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta rika amfani da barazana da dokar ta-baci.
Ta ce ganin yadda gwamnatin ta ci nasara a jihar Ribas, sauran jihohi da masu rike da zababbun mukamai, kamar ‘yan majalisa, na cikin barazana.

Asali: Facebook
Naja’atu Muhammad ta yi wannan bayani ne cikin wata hira da Premier Radio, wacce aka wallafa a shafin Facebook, kan dokar ta-baci da dakatar da gwamnatin jihar Ribas da Tinubu ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa akwai jihohin da gwamnatin tarayya ke ganin dole sai ta mamaye su domin bai wa Bola Ahmed Tinubu damar ci gaba da mulkin kasar nan.
Kano: Naja’atu ta zargi Tinubu da hararar jihohi
Hajiya Naja’atu Muhammad ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin kakaba dokar ta-baci a jihar Kano a kwanakin baya.

Asali: Facebook
Ta ce:
"Kano ma abin da suka so su yi ke nan. Shi ya sa suka sa akwai Sarkin jihar Kano, akwai Sarkin gwamnatin tarayya."
"Idan ka na jin labarin yadda ake zuzuta rigima a kan sarakuna, waye ke tayar da rigima? Waye ke tayar da hankula? Waye ya damu, alhalin mutanen Kano suna harkar cinikayyar su, suna neman kudinsu?"
Naja’atu ta fadi dabarar gwamnati a Kano
Ta kara da cewa gwamnatin tarayya na kokarin ruruta rikicin masarautar Kano saboda wata manufa ta siyasa da ke da alaka da Tinubu.
Naja’atu ta ce:
"Abin da zai faru shi ne, yawancin ‘yan siyasar mu dama can mutanen banza ne. Ba su da wata akida ta alheri ga talaka. Mafi yawansu babu ruwansu da talaka."
Ta yi zargin cewa ana iya yin amfani da karfin gwamnati wajen kwace iko da wasu jihohi kamar Kano domin bai wa shugaban kasa damar samun karfi a nan gaba.
Baya ga Kano, ta ce akwai yiwuwar a tsige sanatoci da sauran masu rike da zababbun mukamai domin cimma wani shiri na sake gudanar da zabe.
Dokar ta-baci: Naja’atu ta gargadi ‘yan Najeriya
Fitacciyar ‘yar siyasa a kasar nan ta bukaci ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen hana yunkurin amfani da dokar ta-baci da shugaba Tinubu ya sanya a jihar Ribas.
Ta ce:
"Zai ci gaba da cire gwamnoni, za a cire Sanatan da ba a so. Mun ga yadda aka yi wa Natasha, mun ga yadda aka yi wa Ningi."
Naja’atu ta ce sanya dokar ta-baci da cire zababbun shugabanni raina hankalin ‘yan Najeriya ne da suka fito rumfunan zabe.
Gwamnatin jihar Kano ta yi naɗe-naɗe
A baya, mun wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da jerin sababbin naɗe-naɗe a gwamnatin Kano, inda aka dauko matasa da dama don cike mukamai daban daban.
Daya daga cikin nade-naden da suka fi daukar hankula shi ne na Auwal Lawan Aranposu, wanda aka ba mukamin Mataimakin darekta janar a hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng