Ribas: An Fallasa Yadda Wike da Gwamnatin Tinubu Suka Kitsa Dakatar da Fubara
- Wani babba a Neja Delta ya bayyana dakatar da gwamnan Ribas a matsayin haramtacce kuma an sabawa kundin tsarin mulki
- A cewar Cif Anabs Sara Igbe, Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, na da hannu dumu-dumu a rikicin da ya jawo dakatar da Simi Fubara
- Sara-Igbe ya bayyana cewa an kitsa dokar ta-baci domin raunana gwamnan Ribas da tilasta shi ya mika wuya ga gwamnatin tarayya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Babba a yankin Neja Delta, Cif Anabs Sara-Igbe, ya soki dakatar da Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Ya bayyana cewa dakatar da zababbiyar gwamnati haramtaccen mataki ne wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Asali: Facebook
A hira da ya yi da Arise News a ranar Alhamis, ya yi ikirarin cewa Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, na da hannu dumu-dumu a rikicin siyasar da ke gudana a Rivers.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sara-Igbe ya zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da yin amfani da karfi fiye da wanda kundin tsarin mulki ya ba shi wajen dakatar da zababben gwamna.
Ribas: Sara-Igbe ya fadi illar dokar ta baci
Cif Sara-Igbe ya kuma bayyana cewa ayyana dokar ta-baci a jihar abu ne da aka shirya tun farko don raunana Gwamna Fubara da tilasta shi ya mika wuya.

Asali: Facebook
Sara-Igbe ya soki yadda aka tura jami’an tsaro masu yawa yayin ziyarar Wike a jihar, ya na mai cewa hakan an yi shi ne domin haddasa fargaba da neman halatta dokar ta-baci.
Ya ce:
“Dakatar da Fubara mataki ne da ba bisa doka ba. Kundin tsarin mulki bai bai wa shugaban kasa ikon yin hakan ba.”
“Ministan ya zo Ribas da sojoji, ‘yan sanda, jiragen yaki, DSS, da manyan makamai, duk don wata ziyarar aiki. Manufar ita ce a haddasa tashin hankali domin a sami hujjar ayyana dokar ta-baci.”
Dattijo a Ribas ya caccaki gwamnatin Tinubu
Sara-Igbe ya kuma zargi fadar shugaban kasa da fifita gefe guda a cikin rikicin siyasar Ribas, yana mai cewa Shugaba Tinubu bai dauki mataki kan rawar da Wike ke takawa ba.
A cewarsa:
“Idan kai uba ne kuma ‘ya’yanka biyu su na fada, dole ne ka zama adali a tsakaninsu. Ba za ka hukunta guda ba ka bar dayan, musamman wanda ya haddasa matsalar.”
Dattijon ya jaddada cewa babuu wata doka da ta ba Tinubu damar dakatar da gwamna da aka zaba, yana mai yin nuni da sashe na 182, 183, 188, da 189 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
El-Rufai aika da sako kan batun Ribas
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya janye hukuncin dakatar da zababbun jami’an gwamnati a Jihar Ribas.
Ya bayyana cewa wannan mataki ya sabawa doka kuma barazana ce ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya, saboda haka dole ne a dauki matakin soke dokar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng