Majalisar Wakilai Ta Ɗauki Zafi kan Bukatar Tinubu na Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Ribas
- Ƴan Majalisar Wakilan Tarayya sun fara muhawara kan bukatar shugaban ƙasa, Bola Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas
- Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙar Tinubu a zaman yau Alhamis, 20 ga watan Maris, 2025
- A ranar Talata da ta gabata shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara bayan ayyana dokar-ta-ɓacin saboda abubuwan da ke faruwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar wakilai ta tarayya ta fara tattaunawa kan buƙatar da Bola Ahmed Tinubu ya aike mata na amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.
A zaman yau Alhamis, 20 ga watan Maris, 2025, Kakakin majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya karanta wasikar da shugaban ƙasa ya aike musu.

Asali: Twitter
Jaridar The Cable ta tattaro cewa Tinubu ya buƙaci majalisar da ta gaggauta amincewa da matakin da ya ɗauka a jihar Ribas.

Kara karanta wannan
Tinubu ya jawo wa kansa, dattawan Ribas sun faɗi matsayarsu kan dakatar da gwamna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakan da Bola Tinubu ya ɗauka a Ribas
A ranar Talata ne Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar, ya na mai kafa hujja da rikicin siyasa mai tsawo da ya dabaibaye jihar, wanda ya ce ya yi barazana ga zaman lafiya da tsaro.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa rashin iya shawo kan rikicin siyasar da ke faruwa ya haifar da ɓarkewar matsaloli da suka haɗa da hare-haren da suka lalata kadarorin gwamnati.
Bisa wannan dalili, Shugaba Tinubu ya ce dole ne a ɗauki matakin gaggawa don dawo da doka da oda.
Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamna
A wani mataki mai cike da ruɗani, Tinubu ya sanar da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce daga masana shari’a da ‘yan siyasa, wasu su na mai cewa matakin ya saba wa tsarin mulki.

Kara karanta wannan
Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci
Bayan haka, shugaba Tinubu ya naɗa tsohon shugaban hafsan rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin sabon mai kula da harkokin jihar.
A cewarsa, sabon shugaban riƙo zai tabbatar da zaman lafiya da bin doka, amma ba zai iya kafa sababbin dokoki ba.

Asali: Twitter
Majalisar wakilai ta fara muhawara kan batun
Majalisar wakilai na da mambobi 360, yayin da majalisar dattawa ke da 109.
Shugaba Tinubu na buƙatar akalla kuri’u 240 a majalisar wakilai da kuma 73 a majalisar dattawa domin dokar ta-bacin ta tabbata.
A halin da ake ciki, ana ci gaba da samun rarrabuwar kai tsakanin ‘yan majalisar kan ko ya dace a amince da dokar ta-bacin ko kuma a ƙi amincewa da ita, rahoton Daily Trust.
Wasu ‘yan majalisa, musamman daga jam’iyyun adawa, sun nuna damuwa cewa matakin dakatar da gwamnan da majalisar dokoki na iya zama cin zarafi ga dimokuraɗiyya.
Shugaban riko na Ribas ya yi magana
A wani labarin, kun ji cewa sabon shugaban riko na Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya yi alƙawarin tabbatar da tsaro da bin doka da oda a jihar.
Ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shi a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng