Kiranye daga Majalisa: Sanata Natasha Ta Fadi Abin da Take Tsoro

Kiranye daga Majalisa: Sanata Natasha Ta Fadi Abin da Take Tsoro

  • Natasha Akpoti-Uduaghan ba ta damu ba kan yunƙurin da wasu mutanen mazaɓarta suka fara na yi mata kiranye daga majalisar dattawa
  • Natasha wacce ke wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta ji komai ba kan yunƙurin raba ta da majalisa da aka fara
  • Sanatar da ke wakilici a karkashin PDP ta ce wasu ƴan siyasa suka ɗauki nauyin shirin na yi mata kiranye, kuma ba zai taɓa yin wani tasiri ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi martani kan kiranyen da wasu mutanen mazaɓarta suka fara yi mata.

Sanata Natasha ta bayyana cewa ba ta damu da ƙoƙarin da ake yi na ganin an raba ta da majalisar dattawa ba.

Natasha ta yi martani kan yunkurin yi mata kiranye
Sanata Natasha ta ce yunkurin yi mata kiranye ba zai yi tasiri ba Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Twitter

Sanata Natasha ta bayyana hakan ne ta hannun mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Israel Arogbonlo, a wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Punch ta yi da shi a wayar tarho a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sabuwar barazana ta tunkaro Sanata Natasha kan zamanta a majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotannin sun nuna cewa wasu mutane daga mazaɓar Kogi ta Tsakiya sun fara yunƙurin raba ta da kujerarta a majalisar dattawa.

A yayin aikin wanda aka gudanar a ƙaramar hukumar Okehi a ranar Laraba, an ga wasu masu kaɗa ƙuri’a su na yin rajista don aiwatar da shirin yi mata kiranye.

Wane martani Sanata Natasha ta yi?

Duk da haka, mai taimakawa Akpoti-Uduaghan ya bayyana wannan yunkuri na tsige ta a matsayin wanda wasu suka ɗaauki nauyinsa.

Israel Arogbonlo ya bayyana cewa yunƙurin yi wa Sanata Natasha kiranye daga majalisa ba zai yi tasiri ba.

“Duk abin da ku ke gani, wasu mutane ne masu wata manufa ta ƙashin kansu suka ɗauki nauyinsa. Ba mu da dalilin yin ce-ce-ku-ce da kowa. A ganinmu, wannan yunƙuri ba zai yi tasiri ba."
"Ba mu fuskantar wani nau’in matsin lamba kuma ba za mu taɓa fuskanta ba. Ina fatan kun tuna cewa ƴan mazaɓar mu na gaskiya sun gudanar da zanga-zanga kwanaki biyu da suka wuce, inda suka musanta zargin cewa ana shirin yin kiranye."

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnatin Tinubu ta fadi gatan da za ta yi wa 'shugaban rikon kwarya'

- Israel Arogbonlo

PDP ta soki shirin yi wa Natasha kiranye

Hakazalika, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana shirin yi wa Natasha kiranye, a matsayin abin da aka kitsa don dalilan siyasa.

Ya zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da kasancewa jagororin wannan yunƙuri.

Kotu ta kawo cikas ga Sanata Natasha

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun tarayya da ke Abuja ta kawo cikas ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan taƙaddamar da take yi da majalisar dattawa.

Kotun ta sauya umarnin da ta ba da na hana majalisar dattawa dakatar da sanatar mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya.

Mai shari'a Obiora Egwuatu ya janye umarnin tare da ba da dama ga majalisa ta ci gaba da ladabtar da sanatar da aka dakatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng