Fubara na Iya Dawowa: Tinubu na Fuskantar Barazana kan Dokar Ta Baci a Majalisa
- Dokar ta ɓacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers na ci gaba da jawo cece-kuce sosai a Najeriya
- Shugaba Tinubu na fuskantar ƙalubale wajen samun adadin ƴan majalisar da ake buƙata domin amincewa da dokar
- Idan ba a samu yawan adadin da ake buƙata a majalisun guda biyu ba, hakan na nufin dokar za ta daina aiki gaba ɗaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu na iya samun matsala a majalisa kan dokar ta ɓaci da ya sanya a jihar Rivers.
Shugaba Tinubu na buƙatar ƴan majalisa su amince da sanya dokar ta ɓacin da ya yi a jihar wacce ke da arziƙin mai.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Tinubu na fuskantar babban ƙalubale wajen samun goyon bayan kaso biyu bisa uku na ƴan majalisar tarayya domin amincewa da dokar ta ɓacin.

Kara karanta wannan
Majalisar Wakilai ta ɗauki zafi kan buƙatar Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya sa dokar ta baci a Rivers
A ranar Talata, Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar da ke kudu maso kudu, inda ya kafa hujja da rikicin siyasa da ya addabi jihar.
Shugaban kasa ya dakatar da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokoki na jihar har na tsawon watanni shida, matakin da ya haddasa ce-ce-ku-ce.
Tinubu ya naɗa Ibok-Ete Ibas, tsohon hafsan rundunar sojojin ruwa, a matsayin shugaban riƙo na jihar.
Me kundin tsarin mulki ya ce kan dokar ta ɓaci?
Don dokar ta ɓacin ta fara aiki, sashe na 305 (2) na kundin tsarin mulki ya tanadi cewa dole ne shugaban ƙasa ya aika da sanarwar ga shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai.
Ana ci gaba da muhawara kan ikon shugaban ƙasa na dakatar da gwamnan da aka zaɓa, domin babu tanadin da ya fayyace hakan a kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

Kara karanta wannan
Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci
Har ila yau, babu tanadi na naɗa shugaban riƙo, kodayake tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya buɗe kofar yin hakan a baya.
Sashe na 305 (6) na kundin tsarin mulki ya tanadi cewa sanarwar za ta daina aiki idan ba a samu kaso biyu bisa uku cikin kwanaki biyu ba idan majalisa na aiki, ko cikin kwanaki 10 idan majalisa ba ta aiki.
Tun da akwai ƴan majalisa 360 a majalisar wakilai da 109 a majalisar dattawa, Tinubu na buƙatar aƙalla ƙuri’u 240 a majalisar wakilai da 73 a majalisar dattawa don dokar ta ɓacin ta tabbata.
A ɗaya hannun, ana buƙatar ƙuri’un sanatoci 36 kacal don daƙile dokar ta ɓacin. Ko da majalisar dattawa ta amince, ƴan majalisar wakilai 121 na iya yin watsi da ita.
Shugaba Bola Tinubu na fuskantar ƙalubale
Majiyoyi daga majalisar tarayya sun bayyana cewa magoya bayan shugaban ƙasa na fuskantar jan aiki wajen tattara yawan ƙuri’un da ake bukata.
Sakamakon rashin isassun ƙuri’u, majalisar dattawa ta ɗage muhawara kan batun zuwa ranar Alhamis.
Majiyoyi sun ce da dama daga cikin ƴan majalisa ba su gamsu da sahihancin matakin Tinubu ba, domin suna ganin hakan zai iya zama mummunan misali a gaba.
Wata majiya ta ce ƴan majalisar sun rabu bisa bambancin jam’iyya, inda ƴan adawa da wasu daga cikin ƴan jam’iyyar APC ke kokwanto kan amincewa da dokar ta ɓacin.
Idan shugaban ƙasa ya kasa samun goyon bayan kaso biyu bisa uku na dukkan majalisun kafin ranar Alhamis za a samu matsala.
Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, kenan dole ne Tinubu ya janye sanarwarsa, wanda hakan zai mayar da Fubara da gwamnatinsa kan mulki.
Gwamnatin Tinubu ta faɗi taimakonta ga Fubara
A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta hannun ministan shari'a, Lateef Fagbemi, ta kare matakin da ta ɗauka na sanya dokar ta ɓaci a jihar Rivers.
Lateef Fagbemi SAN ya bayyana cewa sanya dokar ta ɓacin ya tseratar da Gwamna Siminalayi Fubara daga shirin ƴan majalisa na tsige shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng