Abin da Sabon Shugaban Riko na Jihar Ribas Ya Faɗa bayan Ganawa da Bola Tinubu

Abin da Sabon Shugaban Riko na Jihar Ribas Ya Faɗa bayan Ganawa da Bola Tinubu

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon shugaban riko da zai jagoranci Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya)
  • Vice Admiral Ibas, tsohon hafsan sojojin ruwan Najeriya ya yi alkawarin dawo da tsaro da bin doka da oda a jihar Ribas
  • Ya ce ya fahimci yanayin da ya kai ga naɗa shi a wannan muƙamin kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen ceto Ribas daga matsalar da ta shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sabon shugaban riko na Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya bayyana kudirinsa na tabbatar da doka da oda a jihar da ke fama da rikici.

Vice Admiral Ibas ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro, bin doka da daidaito a jihar Ribas da ke fama da rigingimu da suka ƙi ci su ka ƙi cinyewa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya maida martanin barazanar dakatar da shi kamar yadda aka yi a Ribas

Tinubu da Ibas.
Sabon Shugaban riko na jihar Ribas ya yi alkawarin dawo da tsaro da daidaito Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya rantsar da shugaban riƙon Ribas

Shugaban rikon ya yi wannan jawabi ne da yake zantawa da masu ɗauko rahoto a fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu, cewar rahoton Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da tsohon hafsan rundunar sojin ruwa ta Najeriya, Ibas a matsayin shugaban riko wanda zai kula da lamurran Ribas na wani lokaci.

Jim kaɗan bayan karɓar rantsuwar kama aiki a fadar shugaban kasa, Vice Admiral Ibas ya yi alkawarin tabbatar da tsaro a Ribas.

Jawabin da Ibas ya yi bayan rantsuwa

"Mun fahimci yanayin da ya kawo mu wannan matsayi kuma mai girma shugaban ƙasa ya yi bayanai a jawabin da ya yi kai tsaye.
"Idan batun da ke gabanmu shi ne tabbatar da doka da oda a jihar, to wannan ne babban aikin da ya rataya a kaina ko zan tasa shi domin kowane irin ci gaba ya samu a Jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

Tsohon hafsan rundunar sojin ruwa ya yi alkawarin yin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali ga al’ummar jihar Ribas da Najeriya baki daya.

Rikicin Ribas: Matakan da Tinubu ya ɗauka

A ranar Talata, 18 ga Maris, 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya kuma sanar da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Tinubu ya danganta matakin da ya dauka da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, yana mai cewa ba zai zura ido yana kallon rikicin siyasa na ƙaruwa ba tare da daukar mataki ba.

Bola Tinubu da Fubara.
Bola Tinubu ya dauki matakan shawo kan rigingimun jihar Ribas Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Nan take, Shugaban Kasa ya nada Ibas, tsohon hafsan rundunar sojin ruwa na Najeriya daga 2015 zuwa 2021, a matsayin sabon shugaban riƙo na jihar mai arzikin mai.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

Sai dai dakatar da Fubara da sauran zababbun wakilai ya jawo ce-ce-ku-ce, inda manyan ‘yan Najeriya, kwararrun lauyoyi, da kungiyoyi da dama suka yi tir da matakin.

A yanzu dai shugaban ƙasa ya rantsar da shugaban riƙo da ya naɗa a Ribas kuma ya yi alkawarin dawo da tsaro da bin doka da oda.

Bola Tinubu ya ceci Fubara daga tsigewa

A baya, kun ji cewa Antoni Janar na Tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya ce Bola Tinubu ya ceci Simi Fubara daga tsigewa da ya dakatar da shi.

Ministan ya ce da ba don dokar ta-baci ba da gwamnatin Tinubu ta sanya ba da tuni an tsige Gwamna Simi Fubara daga kujerarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng