Dakatar da Fubara: Gwamnonin PDP Sun Fusata, Sun Fadi Kuskuren Tinubu

Dakatar da Fubara: Gwamnonin PDP Sun Fusata, Sun Fadi Kuskuren Tinubu

  • Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP sun nuna rashin gamsuwarsu kan dakatarwar da aka yi wa Siminalayi Fubara
  • A cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar gwamnonin na PDP, ya soki matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers
  • Gwamna Bala Mohammed ya nuna cewa dakatarwar babbar barazana ce ga dimokuraɗiyya ƙasar nan
  • Ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta janye matakin na zalunci domin cike yake da kura-kurai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi martani kan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Gwamnonin na PDP sun sha alwashin ƙalubalantar dakatarwar da aka yi wa Gwamna Fubara, da sauran zaɓaɓɓun jami’an jihar a gaban kotu.

Gwamnonin PDP sun caccaki Tinubu
Gwamnonin PDP sun ce Tinubu ya yi kuskure kan dakatar da Gwamna Fubara Hoto: @OfficialPDPNig, @DOlusegun
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed ya rattaɓawa hannu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An gano inda Gwamna Fubara yake bayan sojoji sun mamaye fadar gwamnatin Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, ya dakatar da gwamnan, mataimakiyarsa, da mambobin majalisar dokokin jihar Rivers.

Me gwamnonin PDP suka ce kan dakatar da Fubara?

A cikin sanarwar, gwamnonin na PDP sun buƙaci shugaba Tinubu da ya amince cewa ya yi kuskure kuma ya janye wannan hukuncin da ya yanke, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

Gwamnonin sun zargi shugaban ƙasan da nuna son rai, suna mai cewa ya kasa yin magana kan rawar da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ke takawa wajen tayar da rikicin siyasa a jihar Rivers.

“Mu na tare da Gwamna Siminalayi Fubara da jama’ar jihar Rivers a wannan mawuyacin lokaci a tarihin siyasar jihar."
“Duk wanda ke neman adalci dole ne ya kasance mai gaskiya. Shugaban ƙasa, shiru da kake kan rawar da ministan Abuja ya taka a wannan rikici ya nuna cewa ka na goyon bayansa."

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Manyan zunubai 3 da Tinubu ya nuna Gwamna Fubara ya aikata

"Ya mayar da kansa doka mai zaman kanta domin yana aiwatar da umarninka. Yanzu mun gane. Wannan bai dace ba, son kai ne da haddasa rarrabuwar kai."
“Mu na bayyanawa a fili cewa wannan hari da aka tsara da gangan kan jihar Rivers, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa, shi ne mafi girman barazana ga dimokuraɗiyya a ƙasar mu a yau."
“Saboda haka, muna kira ga shugaban ƙasa da ya saurari shawarwari masu kyau, kuma ya amince cewa ya aikata babban kuskure sannan ya gaggauta janye wannan matakin zaluncin kafin lokaci ya ƙure."

- Gwamna Bala Mohammed

Atiku ya yi martani kan dakatar da Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi martani kan dakatarwar da Shugaban kasa ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na PDP, ya bayyana cewa matakin da Bola Tinubu ya ɗauka cike yake ɗa wata manufa ta siyasa.

Kara karanta wannan

An jero abubuwa 2 da El Rufai zai yi amfani da su wajen karya Tinubu da APC a 2027

Atiku ya zargi shugaban ƙasan da cewa yana da hannu dumu-dumu a cikin rikicin siyasar da ke aukuwa a jihar Rivers.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng