Gwamna Nwifuru Ya Ɗauki Zafi, Ya Sallami Hadimai 2 da Aka Gano Sun Yi Rashin Kunya
- Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru ya yi suna wajen rashin daukar aiki da wasa, kori hadimansa guda biyu daga aiki bisa laifin rashin ladabi a bakin aiki
- Sakatariyar gwamnatin jihar Ebonyi, Farfesa Grace Umezurike ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 18 ga watan Maris 2025
- Gwamnan ya gargaɗi dukkan jami'an gwamnati cewa ba zai lamunci sakaci a bakimnaiki ko saba dokoki da ƙa'idojin da aka shinfiɗa a gwamnatinsa ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi - Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya sallami hadimansa guda biyu bisa zargin aikata manyan laifukan rashin da’a da cin amanar aiki.
Wannan matakin ya zo ne a lokacin da gwamnan ke kokarin tsaftace shugabanci tare da tabbatar da cikakken bin doka da oda a tsakanin jami’an gwamnati.

Asali: Facebook
Gwamna Nwifuru ya kori masu taimaka masa ne bayan tabbatar da sun aikata laifuffukan da suka shafi rashin ɗa'a a wurin aiki, kamar yadda The Nation ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimai 2 da Gwamna Nwifuru ya kora
Hadiman da gwamnan ya kora sun haɗa da Mr. Nnanna Nwangele, mai taimaka wa gwamna na musamman kan harkokin tsaron filayen jiragen sama.
Sai kuma Mr. Felix Okemini, babban mataimakin gwamna na musamman kan harkokin tsaro a yankin Ebonyi ta Arewa.
Sakatariyar gwamnatin jihar Ebonyi, Farfesa Grace Umezurike ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 18 ga watan Maris, 2025.
Ta ce an tabbatar da cewa sallamar hadiman gwamnan ne bayan gano wasu manyan laifuffuka da suka aikata wadanda suka sabawa ka’idojin aiki a gwamnatin jihar.
Gwamna Nwifuru ya umarci su bar ofis
Sanarwar ta kara da cewa an umarci wadannan jami’ai su mika duk wata dukiyar gwamnati da ke hannunsu ga ofishin sakataren gwamnatin jihar kafin karfe 4:00 na yamma a yau Talata.
"Tun daga yau, wadannan jami’ai ba su da ikon kasancewa a kusa da fadar gwamnatin jihar Ebonyi ko kuma shiga kowace irin harkar gwamnati," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan
Kwamishinoni 3 sun kai gwamna wuya a wurin taro, Nwifuru ya ɗauki mataki mai tsauri
Wannan matakin na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da gwamnan ya dakatar da kwamishinoni uku bisa laifin rashin halartar taron majalisar zartaswa ba tare da izini ba.
An dakatar da kwamishinoni 3 a Ebonyi
Kwamishinonin da aka dakatar sun hada da: kwamishinan tallafi ɗa harkokin jin ƙai, Solomon Azi, kwamishinan muhalli, Victor Chukwu da kwamishinan raya karkara.
An dakatar da su na tsawon wata guda sakamakon rashin halartar taron majalisar da aka gudanar a ranar Litinin ba tare da wani dalili mai gamsarwa ba.
Gwamna Nwifuru ya yi gargadi ga dukkan sauran jami’an gwamnati da cewa ba zai lamunci sakaci da aiki ba.
Ya kuma ƙara nanata cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka dace domin inganta jin dadin al’ummar jihar Ebonyi.
Gwamnan Ebonyi ya dawo da kwamishinoni
A wani labarin, kun ji cewa bayan tsawon lokaci, Gwamna Francis Nwifuru ya dawo da kwamishinoni uku da ya dagatar ciki har da kwamishinan ƙananan hukumomi.
Gwamnan ya kuma dawo da babban sakataren ma’aikatar Lafiya da shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko, ya umarci su ci gaba da aikinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng