Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Kasa Hakura, Ta Sake Sabuwar Fallasa kan Akpabio
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ƙara ba da haske kan zargin da take yi wa Godswill Akpabio na yunƙurin yin lalata da ita
- Ta bayyana cewa har a zauren majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya taɓa nuna mata alama da ke nuna yana son ta ba shi dama
- Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi mata daga majalisa, an yi ta ne domin toshe mata baki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ci gaba da haƙiƙancewa kan zargin lalata da take yi wa Godswill Akpabio.
Sanata Natasha ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya taɓa yunƙurin nuna mata maitarsa a fili a zauren majalisar.

Asali: Facebook
Sanata Natasha ta bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da ita wacce da tashar BBC Hausa ta sanya a ranar Talata, 18 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan
"Majalisa ta koma kamar kungiyar asiri," Natasha ta fadi abin da Sanatoci ke tsoro
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ko Akpabio ya taɓa yunƙurin neman Natasha a majalisa?
A yayin hirar, an tambaye ta ko da gaske Akpabio ya yi yunƙurin nemanta a cikin zauren majalisar dattawa.
Sanata Natasha ta bayyana cewa akwai wani lokaci ta manta da saka zoben aurenta domin zuwa wurin aiki, sai Akpabio ya yi yunƙurin nuna mata maitarsa a fili.
"Akwai lokacin da ina saurin zuwa wurin aiki sai na manta da sanya zobena. Akwai kimanin sanatoci biyar a wurin."
"Sai ya ce, ‘to Natasha, ba ki saka zobenki ba, shin hakan wata hanyar gayyata ce da za ki ci amanar mijinki?’ Kun san, kalamai irin waɗannan dai."
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan dai an dakatar da ita daga majalisar dattawa a ranar 6 ga watan Maris saboda zargin rashin ɗa'a.
Sai dai, Sanata Natasha ta danganta dakatarwar da aka yi mata kan abin da ta bayyana a matsayin zargin da ta yi wa Akpabio na yunƙurin cin zarafinta.
Ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi mata wata hanya ce da ake son bi domin toshe mata baki.
Yadda Akpabio ya 'nemi' Natasha a gidansa
"Ina fuskantar azabtarwa. Dakatar da ni wata hanya ce ta toshe bakina."
"Abubuwan sun faru lokaci bayan lokaci. Muna a gidansa. Yana nuna min ɓangarorin gidansa. Mijina yana tafiya a bayanmu, shi kuma yana riƙe da hannuna."
"Ya matsa hannuna da wata alama da ke nuna sha'awa. Mu mata mun san abin da hakan ke nufi idan namiji ya matsa hannunmu da wata ma’ana."
"Sai ya ce, 'yanzu kin shigo majalisar dattawa, zan sama mana lokaci domin mu dinga zuwa nan mu ji daɗi'. Kun gane ai, irin hakan dai."
- Natasha Akpoti-Uduaghan
Majalisa ta musanta zargin Natasha
Sai dai mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar tattawa, Onyekachi Nwaebonyi, ya musanta waɗannan zarge-zarge, yana mai cewa Akpabio bai taɓa yin wani yunƙuri na yin lalata da ita ba.
Har ila yau, ya ƙaryata iƙirarin da ta yi cewa majalisar ta na ƙoƙarin toshe mata baki, yana mai jaddada cewa ayyukanta na majalisa sun nuna akasin haka.
Sanata Natasha ta zargi jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi jami'an tsaron Najeriya da yunƙurin cafke ta.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi zargin cewa za a cafke ta ne da zarar ta dawo gida Najeriya daga ƙasar Amurka bayan ta halarci taron IPU.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng