"Majalisa Ta Koma Kamar Kungiyar Asiri," Natasha Ta Fadi Abin da Sanatoci ke Tsoro
- Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce 'yan majalisa na tsoron fadar ra'ayin da ya saba da na sauran saboda fargabar ramuwar gayya
- Ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke zaman gida, bayan majalisar dattawan ta dakatar da ita bisa zargin take dokokin zauren
- Kan zargin da ta yi wa Sanata Godswill Akpabio, Sanatar ta ce shugaban majalisar ya nuna alamun nemanta a wurare da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta ce majalisar dattawa ta Najeriya kamar “ƙungiyar asiri” ce.
Ta ce ta fadi haka ne saboda ba a yarda Sanata ya fito da ra’ayin da ya saba wa na sauran ‘yan majalisa saboda tsoron ramuwar gayya.

Kara karanta wannan
"Gwamnatin Najeriya na shirin kama ni": Sanata Natasha ta fadi halin da take ciki

Asali: Facebook
A hirar da ta kebanta ga BBC, Natasha ta bayyana hakan ne a lokacin da take magana kan dakatar da ita daga majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya faru ne bayan da ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da neman cin zarafinta.
An dakatar da Sanata Natasha daga majalisa a ranar 6 ga Maris bisa zargin “rashin ɗa’a”, bayan wata takaddama da ta yi da Akpabio kan wurin zaman ta a majalisa.
Natasha Akpoti ta soki hukuncin majalisa
Sanata Natasha ta ce an ɗauki matakin dakatar da ita daga majalisa ne domin a hana ta yin magana, tare da nuna cewa an zalunce ta.
Ta ce:
"Ana cutar da ni. An dakatar da ni ne don a hana ni magana."

Asali: Facebook
A karin bayaninta kan yadda Sanata Godswill Akpabio ya rika kokarin nemanta, ta bayyana cewa ya rika amfani da damarsa wajen fada mata maganganu.
Ta ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan
Natasha: Kungiyar 'yan majalisun duniya ta karbi koken Sanata, za ta ji ta bakin Akpabio
"Yana faruwa lokaci bayan lokaci, mataki bayan mataki. Mun kasance a gidansa, ya na zagaya da ni a cikin gidansa. Mijina yana biye da mu a baya. Ya rike hannuna."
"Sai ya matse hannuna da wata alama mai nuna wani abu. Mu mata mun san abin da hakan ke nufi idan namiji ya matse hannunmu da wata manufa."
"Daga nan sai ya ce, ‘Tun da yanzu kina majalisa, zan samar da wata dama mu zo nan mu rika huta wa, kin fahimta dai.'”
Cin zarafi: Natasha ta kafe kan zargin Akpabio
Da aka tambaye ta ko Akpabio ya taɓa yunkurin nemanta a cikin majalisa, Sanata Natasha ta ce akwai wani lokaci da ya tambayeta ko tana gayyatar su neme ta nw saboda ba ta sa zoben aurenta ba.
Ta ce:
"Wata rana na yi sauri zuwa aiki na manta ban sa zoben aure na ba. Akwai kimanin sanatoci biyar a wajen. Sai ya ce, ‘Oh Natasha, ba ki sa zobenki ba, shin wannan gayyata ce? Ko ba dama’
Majalisa ta kare Akpabio daga zargin Natasha
Da yake mayar da martani kan wannan zargi, Onyekachi Nwaebonyi, mataimakin bulaliyar majalisar dattawa, ya ce wani lokaci da Akpabio ya taɓa yin yunkurin neman Natasha.
Ya kuma ce shugaban majalisar bai taɓa yin wata magana da ba ta dace ba ga Sanatar, ko a gidansa ko a zauren majalisa ba
Bugu da ƙari, Nwaebonyi ya ƙaryata ikirarin Sanata Natasha cewa majalisa na ƙoƙarin hana ta magana.
Ya ce:
"Ayyukan Sanata Natasha a majalisa sun nuna cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne."
Sanata Natasha ta zargi majalisa da zalunci
A baya, mun kawo labarin cewa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi mata zalunci ne.
Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha bisa zargin ɓata suna da rashin da’a, bayan wani musayar yawu mai zafi da ta yi da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng