Kwamishinoni 3 Sun Kai Gwamna Wuya a Wurin Taro, Nwifuru Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri

Kwamishinoni 3 Sun Kai Gwamna Wuya a Wurin Taro, Nwifuru Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri

  • Gwamna Francis Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni daga aiki na tsawon wata guda saboda rashin halartar taron majalisar zartarwa
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ebonyi, Jude Okpor ne ya sanar da hakan, ya ce an dakatar da su ne saboda ba su nemi izini ba
  • Majalisar zartarwa ta amince da ware wasu maƙudan kudi domin gudanar da ayyuka a sansanin NYSC da karrama wasu ɗalibai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya dakatar da kwamishinoni uku daga aiki na tsawon wata guda saboda rashin halarta taron majalisar zartarwa.

Gwamna Nwifuru ya ɗauki wannan mataki ne bayan kwamishinonin sun yi fashin taron kuma ba tare da sun yanki wani uzuri ba.

Gwamna Nwifuru.
Gwamnan Ebonyi ya dakatar da kwamishinoni 3 bisa rashin halartar taro ba tare da izini ba Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Facebook

Kwamishinoni 3 da gwamna ya dakatar

Jaridar Leadership ta tattaro cewa kwamishinonin da abin ya shafa sun hada da kwamoshinan tallaffi da harkokin jin ƙai, Solomon Azi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauko tsohon kwamishinan Kwankwaso, ya naɗa shi a muƙami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran su ne kwamishinan muhalli, Victor Chukwu da kwamishinan harkokin raya karkara, Ikeuwa Omebe.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ebonyi, Jude Okpor ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron Majalisar Zartarwa.

A cewar Jude Okpor, gwamnan ya yanke wannan hukunci ne don nuna rashin amincewa da halin ko-in-kula da wasu jami’an gwamnati ke yi.

Gwamna Nwifiru ya gargaɗi jami'an gwamnati

Mista Okpor ya ce Gwamna Nwifuru ya gargadi duk wani jami'in gwamnati da ke sakaci da aikinsa, yana mai cewa hakan ba zai daga darajar jihar ba.

Haka kuma, Gwamnan ya umarni kwamishinonin su ajiye duk wasu kayayyaki na alfarma da gata da ke hannunsu wanda ya kasance mallakin gwamnati.

Bayan haka, Nwifuru ya gargadi dukkan ‘yan kwangilar da ke gudanar da ayyukan gwamnati a jihar da su hanzarta kammala aikinsu kamar yadda ak yi yarjejeniya.

Ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen daukar matakan doka kan duk wanda ya ki bin ka’idar kammala aiki a lokacin da aka amince da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun fara lallaba gwamnati, ana son hana kananan hukumomi kudinsu

Abbubuwan da Majalisar ta amince da su

A wani bangare na taron, majalisar ta amince da aiwatar da wasu ayyuka a sansanin bai wa matasa masu yi wa kasa hidima watau NYSC da ke Afikpo.

Daga cikin ayyukan da Gwamnatin Nwifuru za ta yi a sansanin NYSC har da gina gidajen ma'aikata, ɗakunan kwann mata da asibitin kula da lafiya.

Haka kuma, Majalisar ta ware Naira miliyan 40 domin gina babban wurin ajiyar ruwa wanda ma’aikatar albarkatun ruwa za ta jagoranta.

Gwamna Nwifuru.
Gwamnatin Ebonyi ta karrama daliban da suka ci gasar shari'a ta duniya Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Twitter

Bugu da kari, Gwamnati ta karrama wasu daliban sashin shari’a na Jami’ar Ebonyi da suka yi nasara a gasar shari’a ta Christ of Heyns African Moot Court Competition da aka gudanar a Kigali a kasar Rwanda a shekarar 2024.

Wadannan dalibai su ne, Michael Agu-Ebeke, Ibor Cynthia Nwamaka da jagoransu Dr. (Mrs) Chioma Vivian Iteshi

Wannan tawaga ita ce ta farko daga wata jami’a a Najeriya da ta yi nasarar lashe wannan gasa cikin shekaru 33.

Kara karanta wannan

Albashi N500,000: 'Yan kasar Sin suka shigo Najeriya, sun kafa kamfanin sarrafa lithium a Nasarawa

Gwamna Nwifuru ya halarci taron ɗan LP

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru ya halarci taron rabon tallafi na ɗan Majalisar Tarayya na LP duk da suna da banbancin jam'iyyun siyasa.

Gwamna Nwifuru na APC ya ce ya zo wurin taron ne domin ya kara fito da ma'anar cewa siyasa ba gaba ba ce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng