El Rufai Ya Fasa Ƙwai: An Ji Dalilin Uba Sani na Korar Shugaban Hukumar KADIRS

El Rufai Ya Fasa Ƙwai: An Ji Dalilin Uba Sani na Korar Shugaban Hukumar KADIRS

  • Mallam Nasir El-Rufai ya fallasa dalilin da ya sa Gwamna Uba Sani ya kori Dr. Zaid Abubakar daga shugabancin hukumar KADIRS a Kaduna
  • A ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023, Gwamnatin Uba Sani ta sanar da nadin Jerry Adams a matsayin shugaban KADIRS bayan korar jami'in
  • Tsohon gwamnan, ya fito ya ce Uba Sani ya kori Dr. Zaid ne saboda ya fara matsin lamba ga kakakin majalisar Kaduna ya biya haraji kan N10bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya sake yin wata bankada game da sha'anin mulkin Gwamna Uba Sani.

A wannan karon El-Rufai ya fallasa dalilin da ya sa Uba Sani ya kori Dr. Zaid Abubakar daga matsayin shugaban hukumar KADIRS.

El-Rufai ya yi magana kan dalilin gwamnatin Kaduna na korar shugaban hukumar KADIRS
El-Rufai ya yi ikirarin cewa an tsige shugaban KADIRS saboda kakakin majalisar Kaduna ka da ya biya haraji. Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

Legit Hausa, ta rahoto cewa, KADIRS, ita ce hukumar da ke da alhakin tarawa da kuma lissafa duk wani kudin shiga da gwamnatin jihar Kaduna ke samu a cikin jihar da wajenta.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 2, Buba Galadima ya fadi wanda ya yi nasara a zaben Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin Dr. Zaid a matsayin shugaban KADIRS

A ranar 18 ga watan Yulin 2019, tsohon gwamna, El-Rufai ya nada Dr. Zaid Abubakar a matsayin shugaban KADIRS, inji sanarwar gwamnatin Kaduna a shafinta na Facebook.

A cikin wata sanarwa da Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, ya fitar, an ji cewa:

"Kafin nadinsa, Dr. Zaid Abubakar ya kasance mai binciken haraji a hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS), wanda ya nuna kwarewa a aikinsa.
"Bisa tanadin dokar hada-hadar haraji ta jihar Kaduna, majalisar dokokin jihar ta tabbatar da naɗinsa a matsayin shugaban hukumar KADIRS."

Uba Sani ya sauke Zaid, ya nada Jerry Adams

Gwamnatin Kaduna, ta shafinta na X, ta sanar da cewa Gwamna Uba Sani ya amince da nadin Kwamared Jerry Adams a matsayin sabon shugaban hukumar KADIRS.

Uba Sani ya kori Dr. Zaid Abubakar daga wannan mukami tare da maye gurbinsa da Jerry Adams, kamar yadda sanarwar ta nuna a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

'Yadda Ribadu ya hada kai da ICPC domin kai ni kurkuku kafin zaben 2027' - El-Rufai

Sai dai, gwamnatin Kaduna, ba ta fito a hukumance ta bayyana dalilin ko an kori Dr. Zaid saboda wata matsala ba, amma ta ce an nada Jerry, saboda kwarewarsa.

El-Rufai ya fallasa dalilin korar shugaban KADIRS

El-Rufai ya fadi dalilin Gwamna Uba Sani dalilin korar shugaban KADIRS
Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai. Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

To sai dai, a hirarsa da Freedom Radio Kano, Mallam Nasir El-Rufai ya ce Gwamna Uba Sani ya tsige Dr. Zaid ne saboda wani bincike da ya fara yi.

"An cire shi, saboda Liman (Yusuf Dahiru Lman), shugaban majalisa, an ce ya biya haraji, domin yana da kudi kusan Naira biliyan 10 da bai biya masu haraji ba, Zaid ya ce sai ya biya, shi ya sa aka cire shi.
"Rahoton ma idan ka tsaya ka kalle shi, ba abin da ke ciki, karairayi ne, da iskanci, da sauransu, kuma, mu da sauran wadanda aka yiwa sharri da wannan rahoton, mun riga mun yi Allah ya isa, za ka ga yadda za su kare."

Kara karanta wannan

El Rufai ya tuno shekaru 8 na mulkinsa, ya fadi abubuwa 4 da ya fi jin dadinsu

Tsohon gwamnan ya ce gwamnatin Uba Sani na jin tsoron a shiga kotu a yi shari'a kan zarge-zargen rashawa ta take yiwa tsohuwar gwamnatinsa, saboda ta san duk 'karya ne.'

Kalli hirar da aka yi da El-Rufai a nan kasa:

El-Rufai ya tuno da shekaru 8 na mulkin Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ce bai yi da na sanin korar dubunnan malaman makaranta a lokacin da yake gwamna ba.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da ya ke bayyana wasu abubuwa hudu da ya fi jin dadinsu a shekaru takwas da ya yi a kan mulkin, ciki har da dawo da ruwan famfo a Zaria.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.