KADIRS: Yadda Gwamnatin El-Rufai ta bunkasa kudin shigan Jihar Kaduna

KADIRS: Yadda Gwamnatin El-Rufai ta bunkasa kudin shigan Jihar Kaduna

Daga shekarar 2015 zuwa 2019, kudin shiga watau IGR da gwamnatin jihar Kaduna ta ke samu ya karu daga Naira biliyan 11 zuwa kusan biliyan 15.

Wannan kokari da jihar Kaduna ta yi ya sa gwamna Malam Nasir El-Rufai ya kerewa duk wasu jihohin Arewa face babban birnin tarayya, Abuja.

Rahotannin da su ka fito daga hukumar tara alkaluma na kasa ta NBS sun nuna cewa Kaduna ce ta shida a Najeriya wajen samun kudin shiga.

A 2015 ne gwamnatin jihar Kaduna ta fara ganin sauyi a asusun kudin shigar ta bayan Nasir El-Rufai ya zama gwamna a karkashin jam’iyyar APC.

Shugaban KADRIS mai alhakin tara kudin shiga a Kaduna, Zaid Abubakar, ya shaidawa Daily Trust cewa duk shekara asusun jihar ya na kumbura.

Dr. Zaid Abubakar ya bayyana cewa tsakanin 2011 zuwa 2015, abin da jihar Kaduna ta ke samu duk shekara a matsayin IGR bai wuce N9b zuwa N12b.

KU KARANTA: Jihohi 6 su na bukatar Dala miliyan 180 inji hukumar WFP

KADIRS: Yadda Gwamnatin El-Rufai ta bunkasa kudin shigan Jihar Kaduna
Gwamna Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Naira biliyan 44.9 da Kaduna ta tara a 2019 shi ne mafi yawan IGR da aka samu a tarihin jihar cikin shekaru 50 kamar yadda Dr. Abubakar ya bayyana.

Bayan hawan El-Rufai gwamna, ya nada tsohon shugaban FIRS na kasa, Ifueko Omoigui-Okauru domin ya gyarawa hukumar jihar ta KADIRS zama.

Kwalliya ta biya kudin sabulu inda a 2016, jihar Kaduna ta tara N23b, a 2017 da 2018 gwamnatin jihar ta kuma samu N26.5 da N29b a asusun ta na IGR.

KADIRS ta yi hasashen samun Naira biliyan 43 a shekarar bara, amma a karshe sai da jihar ta tashi da Naira biliyan 44.9, fiye da abin da aka yi tunani.

Dr. Zaid Abubakar wanda ya zama shugaban KADIRS ya 2019 ya bayyana cewa jihar ta kai matsayin da ta kai a yau ne bayan ta bude fika-fikanta.

A yau Legas. Ribas, Abuja, Ogun da jihar Delta ne kadai su ka sha gaban Kaduna a bangaren IGR.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel