Wike Ya Soke Takardun Filaye kusan 5000, An Fadi Sharadin Mayar Wa Jama'a Dukiyarsu
- Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya amince da soke takardun mallakar filaye 4,794 saboda rashin biyan harajin ƙasa
- Hukumar gudanarwar Abuja ta ce sai da ta ja kunnen jama'a ta hanyar an sanar da masu filaye su biya bashin harajin da ake binsu
- Amma gwamnatin ta bayar da wa’adin ga wadanda abin ya shafa a tsakanin shekara guda zuwa 10 don sake mallakar dukiyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya amince da soke takardun mallakar filaye 4,794 saboda rashin biyan harajin ƙasa na sama da shekaru 40.
A yankunan Central Area, Garki I da II, Wuse I da II, Asokoro, Maitama, da Guzape, jimillar masu filaye 8,375 ba su biya harajin ƙasa ba cikin shekaru 43 da suka wuce.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an yi bayanin ne a taron manema labarai da Mataimakin Musamman na Minista kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa ta Zamani, Lere Olayinka, ya jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lere Olayinka ya samu rakiyar daraktan filaye na hukumar kula da babban birnin tarayya, Abuja, Chijioke Nwankwoeze, don sanar da matakin da aka dauka a kan kadarorin.
Wike: "An ba jama'a damar biyan haraji"
Daily Post ta ruwaito cewa hadimin Ministan ya fadi yadda hukumar gudanarwar Abuja ta sanar a jaridun ƙasa da kafafen watsa labarai tun daga shekarar 2023 kan biyan kudin.
Sai dai ya bayyana takaicin cewa duk da irin ƙoƙarin da aka yi, masu kadarorin sun yi biris da lamarin, kuma kalilan ne daga cikinsu su ka biya kudin.
Ya ce:
“Yana da muhimmanci a fahimta cewa dokokin kasa sun tanadi biyan harajin ƙasa kan filaye da ke Abuja.
An bayyana hakan a cikin sharuɗɗan bayar da takardar mallaka, kuma wajibi ne a biya harajin a ranar 1 ga watan Janairu na kowace shekara."
Unguwannin Abuja da ba a biyan haraji
An tattara jerin sunayen filayen da ke da basussukan harajin ƙasa a cikin yankuna 10 mafi tsufa na matakin farko na Babban Birnin Tarayya.
Yankunan sun haɗa da: Central Area District, Garki I, Wuse I, Garki II, Asokoro, Maitama, Wuse II, da Guzape.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Har zuwa ƙarshen shekarar 2024 da kuma yau, jimillar N6,967,980,119 ake bin masu filaye 8,375 a matsayin harajin ƙasa.
“Har ila yau, jimillar filaye 4,794 ba a biya harajin ƙasa ba na tsawon shekaru 10 da suka wuce. Ma’ana, a cikin waɗannan yankunan da aka ambata, masu filaye 4,794 sun kasa biyan harajin ƙasa cikin shekaru 10 da suka gabata.”
Wike ya ba ƴan Abuja wa'adin kwanaki 21
Lere Olayinka ya ce rashin biyan harajin filaye ya saba da sharuɗɗan bayar da takardar mallakar fili, bisa tanadin sashe na 28, ƙananan sashe na 5(a) da (b) na dokar amfani da ƙasa.
Ya ce:
“Saboda haka, an soke duk takardun filayen da ke da bashin harajin ƙasa na shekaru 10 ko fiye nan take.
“Haka kuma, an ba wa masu filaye da ke da bashin harajin ƙasa tsakanin shekara guda zuwa 10 wa’adin kwanaki 21 don biyan bashin, in ba haka ba za a soke takardun filayensu.”
Wike ya aika motocin rusau gidajen jama'a
A baya, kun ji cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya jagoranci motoci tare da kutsa wa yankin Gishiri da ke ƙarƙashin Katampe don rushe wasu muhallai.
Wike, wanda aka hango a cikin fushi ya na jan kunnen mutanen yankin, ya bayyana cewa sai da su ka biya diyya da yin tayin sabon matsuguni, amma jama'ar su ka ki karba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng