Wata Sabuwa: Zanga Zanga Ta Barke a Abuja, an Gano Dalili
- Wasu masu rajin kare dimokuraɗiyya sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya watau Abuja a ranar Litinin
- Masu zanga-zangar ta lumana suna adawa ne da dauke zaman kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƙananan hukumomin Benue
- Sun buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta ɗaukar matakin hana ɓangaren shari'a durƙushewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wasu mutane sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja.
Masu zanga-zangar sun gudanar da ita ne daga majalisar tarayya zuwa Kotun Koli, domin nuna rashin jin daɗinsu kan rikicin shari’a da ke faruwa a jihar Benue.

Asali: Original
Jaridar The Cable ta ce masu zanga-zangar, waɗanda suka haɗa da ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, suna ɗauke da kwalaye da rubuce-rubuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rubuce-rubucen suna sukar abin da suka kira ƙwace ikon kotun sauraren ƙararrakin zaɓen ƙananan hukumomin Benue da wasu ƴan siyasa suka yi.
Menene buƙatar masu zanga-zangar?
Sun buƙaci alƙalin alƙalai ta Najeriya, mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, da ta gaggauta sanya baki cikin lamarin tare da kawar da alƙalai masu cin hanci daga ɓangaren shari’a na Najeriya, rahoton The Punch ya tabbatar.
Haka kuma, sun roki shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakin gaggawa domin magance matsalar tare da tabbatar da an yi adalci.
Jagoran masu zanga-zangar Igwe Ude-Umanta ya bayyana cewa:
"Muna nan a yau a matsayin ƴan Najeriya da ke son bin doka da oda. Dimokuradiyyarmu tana cikin hatsari, kuma dole ne mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta ceto ta."
"Muna kuma kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ka da ya zura ido ya bari ɓangaren shari’a durkushe."
"Abin da yake faruwa a Benue ya yi muni a yanzu, domin masu shigar da ƙarar ba su ma shiga cikin tsarin zaɓen ba."
Abin da ke faruwa kan zaɓen Benue
Tun da farko, babban alƙalin jihar Benue, mai shari’a Maurice Ikpembese, ya ba da umarnin mayar da zaman kotun sauraren karar zaben ƙananan hukumomi daga Makurdi zuwa Abuja, saboda dalilan tsaro.
Sai dai, zaman kotun da aka shirya farawa a Abuja a ranar 10 ga Maris ya samu cikas, bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Makurdi ta bayar da umarnin hana yin zaman a Abuja.
Babbar kotun tarayyar ta umarci cewa kotun sauraren ƙararrakin zaɓen ta ci gaba da zaman ta a jihar Benue, saɓanin umarnin da mai shari’a Ikpembese ya bayar tun da farko.
Amma jam’iyyar APC mai mulki ta garzaya zuwa wata babbar kotun tarayya a Abuja don neman a mayar da zaman kotun zuwa Abuja kamar yadda babban alƙalin Benue ya umarta tun farko.
A ranar Juma’a, kotun ta amince da buƙatar APC, ta bada umarnin cewa kotun sauraren ƙararrakin ta ci gaba da zaman ta a NBA House da ke Abuja.
Har ila yau, kotun ta hana kotun sauraren karar ci gaba da zama a jihar Benue.
Gwamnan Benue ya musanta shirin komawa SDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya musanta jita-jitar da ke cewa yana shirin ficewa daga APC zuwa jam'iyyar SDP.
Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana cewa zai ci gaba da zama daram a cikin jam'iyyar APC wacce ta ba shi damar zama gwamna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng