An Samu Gawar Sarkin da 'Yan Bindiga Suka Sace a Abuja bayan Kashe Shi

An Samu Gawar Sarkin da 'Yan Bindiga Suka Sace a Abuja bayan Kashe Shi

  • Rahotanni na nuni da cewa an tsinci gawar wani sarkin gargajiya da aka sace a daji kusa da kauyen Takula tsakanin Abuja da Kaduna
  • Bayanai da suka gabata sun nuna cewa 'yan bindiga sun sace sarkin ne a ranar 11 ga Maris, 2025 kafin daga bisani a gano gawarsa
  • A halin yanzu, an ruwaito cewa jami’an tsaro sun dauki matakan bincike da kokarin cafke masu hannu a kisan gillan da aka masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da cewa an samu karin bayanai kan sace wani basarake da 'yan bindiga suka yi cikin dare a Abuja.

'Yan bindigar sun kai hari ne a wani yanki na Abuja, inda suka kutsa har gidan basaraken suka sace shi tare da tafiya da jikokinsa da wasu mutanen yankin.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun kai hari makaranta ana suhur a Katsina, sun yi kisan kai

Abuja
"Yan bindiga sun kashe sarki a Abuja. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Kwanaki bayan sace shi, mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an samu gawarrsa a wani daji bayan an kashe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka samu gawar sarkin da aka sace

Rahotanni sun nuna cewa an gano gawar Yuda Garba, Dagacin Dagachi da aka sace a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, a cikin wani daji kusa da garin Takula.

Bayanan sirri sun nuna cewa wasu mazauna yankin ne suka ga gawar a dajin Nomadic da ke kusa da Kuyeri, a kan iyakar Kaduna da Babban Birnin Tarayya.

Bayan ganin gawar ta shi, mutanen sun garzaya wajen hukumomi suka sanar da su domin daukar matakin da ya dace.

An tabbatar da mutuwar sarkin

Jami’an tsaro sun garzaya wurin tare da wasu daga cikin mazauna yankin, aka tabbatar cewa gawar dagacin da aka sace ne tun a ranar 11 ga Maris.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi tabargazar sace sarki da dare, an kama mutum 5

Iyalan mamacin sun tabbatar da hakan bayan sun gane gawarsa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da fargaba.

Hakan na nuna yadda 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ke cigaba da kai hare hare birnin tarayya Abuja da kuma bukatar tsaurara matakai.

Sufeton yan sanda
Sufeton 'yan sandan Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jami'an tsaro sun fara bincike

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun dauki matakan bincike domin gano wadanda ke da hannu a kashe sarkin.

Haka kuma, hukumomi sun bayyana cewa suna ci gaba da kokarin ceto sauran mutanen da aka sace tare da marigayin a yayin harin da aka kai.

Jami'an tsaro sun tabbatar wa mazauna yankin cewa za su yi iyakar kokarinsu domin gurfanar da masu hannu a kisan gaban shari’a.

Daga yanzu zuwa kowane lokacin ana sa ran cewa jami'an tsaro za su samu nasarar kwato sauran mutanen da aka sace tare da sarkin da kuma kama masu laifin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka

Sace sarki: An kama mutane 5 a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kama mutane biyar da ake zargi suna da hannu wajen kai harin da ya yi sanadiyyar sace wani sarki a Abuja.

Rahoton Legit ya tabbatar da cewa jami'an tsaro sun kama mutanen ne bayan fara bincike domin gano wadanda suka taimaka wajen kai hari da sace sarkin cikin dare a cikin gidansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel