Ramadan: Alamomin da Musulmi Zai Gane Daren Lailatul Qadr a Kwanaki 10 na Ƙarshe
Lailatul Qadr, wanda ake kira Daren Daraja, dare ne mai cike da rahama, gafara kuma shi ne daren da ya fi kowane alheri a addinin Musulunci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wannan dare ya fi watanni 1,000 daraja kamar yadda Allah S.W.T ya bayyana a cikin Alƙur'ani mai girma, sura ta 97, aya ta uku (Suratul Al-Qadr 97:3).

Asali: Getty Images
Duk da cewa ba a san takamaiman ranar da daren ke faɗowa ba, Annabi Muhammad (SAW) ya umarci a neme shi a goman ƙarshe na watan Ramadan.
A hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito, Manzon Allah (S.A.W) ya kwaɗaitar da neman daren Lailatul Qadari a ranakun mara watau 21 23, 25, 27 da 29 ga Ramadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai alamomi daban-daban da ake gane da Lailatul Qadr. Ga su kamar haka:
1. Daidaiton yanayi (sanyi ko zafi)
Ɗaya daga cikin manyan alamomin da ake gane wannan dare mai daraja ita ce yanayin gari zai kasance matsakaici, ma'ana babu tsananin zafi ko sanyi.
A wani faifan bidiyo na Sheikh Aminu Daurawa da aka wallafa a Facebook, ya ce idan ana tsananin zafi a shekarar to daren zai zo da ni'ima babu wannan tsanani.
Haka zalika ba za a yi tsananin sanyi ba a wannan dare, yanayi zai kasance matsakaici, babu sanyi ko zafi mai tsanani.

Asali: Facebook
"Ana gane daren Lailatun Qadr ta hanyar yanayi, idan ana tsananin zafi a lokacin, to za ka ga a wannan dare babu zafi mai tsanani, haka ma idan sanyi ake yi.
- In ji Sheikh Aminu Daurawa.
Wani matashin malami, Malam Yahuza Abdullahi ya ƙara da cewa bayan sanyi da zafi, ko da iska ake yi a lokacin, za ka ga a daren Lailatun Qadr iskar ta zama mai daɗi.

Kara karanta wannan
EFCC ta cafke Akanta Janar, Ana zargin gwamnatin Bauchi ta wawure Naira biliyan 70
2. Yanayin fitowar rana da safiya
Sheikh Aminu Daurawa ya kara cewa alama ta biyu da ake gane daren Lailatul Qadr ya zo, shi ne rana za ta fito fayau washegari, babu wani dabbare-dabbare a jikinta.
"Washegari za ka ga rana ta fito haka dau, ba alamar cin zana a jikinta, hakan alama ce da ke nuna daren Lailatul Qadr ya wuce a daren da ya gabata," in ji Daurawa.
Babban malamin ya ce maganganun da ake yaɗawa cewa za a yaye maka komai ka hango Ka'aba, ko kare ba zai yi haushi ba, jaki ba zai yi kuka ba duk ba alamun daren ba ne.
3. Natsuwa da amincin Lailatul Qadr
Wasu manyan malamai magabata sun bayyana cewa ana samun aminci da natsuwa a duk daren da Lailatul Qadr ta faɗo a watan Ramadan.
Malam Yahuza ya shaida wa Legit Hausa cewa malaman da suka ce ana samun aminci da natsuwa a wannan dare sun kafa hujja da ayar ƙarshe ta suratul Qadr.

Kara karanta wannan
Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno
"Malamai magabata sun ce ana samun natsuwa, bawa zai ji natsuwa da aminci a wannan dare fiye da sauran darare.
"Sun kafa hujja da ayar karshe a suratul Qadr, inda Allah SWT ke cewa: "Akwai aminci (da natsuwa) a daren har wayewar gari."
- In ji Malam Yahuza.
Hikimar ɓoye daren Lailatul Qadr
Sheikh Aminu Ibrahim Ɗaurawa ya ce hikimar ɓoye wannan dare mai albarka shi ne, ana so mutum ya tashi ya raya dukkan dararen goma ta ƙarshe.
A cewarsa, duk wanda ya raya waɗannan kwanaki 10 to tabbas ya dace da daren Lailatul Qadr domin a ɗaya daga ciki daren ke faɗowa.
Daurawa ya kuma kwaɗaitar da mutane su yawaita yin addu'ar da Manzon Allah SAW ya karantar watau "Allahumma Inni Afuwwun, Tuhibbul Afuwa Fa'afu'anni."
Yadda musulmi zai ribaci goman karshe
A baya, mun kawo maku yadda musulmi zai ribaci kwanaki 10 na ƙarshe a watan Ramadan domin samun falala da garaɓasar da ke ciki.
Ana bukatar kowane Musulmi ya dage da ibada a kwanakin karshen watan Ramadan domin tara lada mai yawa da neman yardar Allah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng