Kebbi: Bakuwar Cuta Ta Bulla a Jami'a, An Samu Asarar Rayukan Dalibai

Kebbi: Bakuwar Cuta Ta Bulla a Jami'a, An Samu Asarar Rayukan Dalibai

  • An shiga jimami a jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi (KSUSTA) bayan ɓullar wata baƙuwar cuta wacce ba a san kowace iri ba ce
  • Cutar ta yi sanadiyyar rasuwar ɗalibai biyar na jami'ar wanda hakan ya ƙara jefa fargaɓa a zukatan sauran mutanen da ke cikin makarantar
  • Magatakardar jami'ar ya tabbatar da rasuwar ɗaliban, ya ƙara da cewa ya tuntuɓi kwamishinan ilmi domin samun mafita kan lamarin
  • Ƙungiyar ɗaliban jami'ar ta KSUSTA ta yi kira ga mahukunta da su gaggauta rufe makarantar domin hana yaɗuwar wannan cutar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Rahotanni sun tabbatar da ɓullar wata cuta da ba a tantance ba a jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi (KSUSTA).

Baƙuwar cutar ta yi sanadiyyar rasuwar ɗalibai biyar a jami'ar KSUSTA da ke Aliero a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Bayan sutale El Rufai, APC ta fadi abin koyi daga Muhammadu Buhari

Bakuwar cuta ta bulla a Kebbi
Bakuwar cuta ta kashe dalibai a jami'ar jihar Kebhi Hoto: UNICEF
Asali: UGC

Baƙuwar cuta ta kashe ɗaliban jami'a a Kebbi

Tashar Channesl TV ta ce wasu ɗaliban jami'ar, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu sun tabbatar da aukuwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaliban sun bayyana cewa mutum huɗu sun mutu a makon da ya gabata, yayin da wani abokin karatunsu ya rasu a ranar Lahadi bayan ya yi rashin lafiya cikin dare.

Wata majiya ta bayyana cewa jami'ai daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ziyarci jami'ar a makon da ya gabata don wayar da kan mutane game da haɗarin cutar sanƙarau.

Duk da haka, ba su tabbatar ko cutar sanƙarau ce ta yi sanadiyyar mutuwar ɗalibai biyu da suka rasu kafin ziyarar ta su ba.

Me mahukunta suka ce kan lamarin?

Da aka tuntuɓi magatakardan jami'ar, Maimaru Alhaji Tilli, ya tabbatar da mutuwar dalibai huɗu bisa ga bayanan jami'ar.

"Eh, ɗalibai huɗu sun mutu bisa ga bayananmu, amma har yanzu ba mu san musabbabin hakan ba."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban jam'iyyar na kasa ya tsage gaskiya kan batun murabus

"Ma'aikatar lafiya ta gargaɗe mu, kuma sun ba da shawarar cewa akwai buƙatar rage cunkoso a ɗakunan kwanan ɗalibai."

- Maimaru Alhaji Tilli

Daliban jami'a sun fara neman ɗauki

Maimaru Alhaji Tilli ya ƙara da cewa ya rubuta wasiƙa zuwa ga kwamishinan ilmi, Isah Abubakar Tunga, don neman shawarwari kan matakan da za a ɗauka don daƙile yawan mace-macen.

Wani shugaban ɗalibai ya kuma tabbatar da mutuwar ɗaliban, ya bayyana cewa ƙungiyar ɗalibai (SUG) ta rubuta wasiƙa ga mahukuntan jami'ar, tana roƙon su rufe makarantar don hana samun ƙarin asarar rayuka.

Cutar zazzaɓin lassa ta ɓarke a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Benue da ke Arewacin Najeriya ta tabbatar da samun ɓullar cutar zazzaɓin lassa.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Yanmar Ortese, ya shaida cewa mutum uku sun rasu sakamakon ɓarkewar cutar da aka samu.

Dakta Yanmar Ortese ya bayyana cewa an samu ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da cutar a cikin shekara huɗu da suka gabata a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng