Zargin El Rufai: Gwamna Uba Sani Ya Yi Martani, Ya Fadi Abin da Ya Sa a gaba

Zargin El Rufai: Gwamna Uba Sani Ya Yi Martani, Ya Fadi Abin da Ya Sa a gaba

  • Gwamnan jihar Kaduna, Mai girma Uba Sani, ya bayyana ƙudirinsa na sauke nauyin da aka ɗora masa na mulki
  • Uba Sani ya nuna cewa babban burin da yake da shi ne ya ga ya hidimtawa mutanen da suka zaɓe shi ya zama gwamna
  • Gwamnan ya jaddada cewa bai da lokacin ɓatawa kan ƙananan maganganu waɗanda ba za su kawo ci gaba ga jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya jaddada ƙudirinsa na gudanar da mulki yadda ya dace.

Gwamna Uba Sani ya nanata cewa burinsa shi ne yin hidima ga jama’ar da suka zaɓe shi, maimakon ya riƙa biyewa ana wasu maganganu marasa amfani.

Uba Sani ya yi wa El-Rufai martani
Uba Sani ya yi martani kan zargin El-Rufai Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne yayin liyafar buɗa da ya shirya tare da masu faɗa a ji a kafofin sada zumunta na Kaduna a gidan gwamnati a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Madalla da hutu ga yan sakandare domin azumin watan Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya yi zargi kan Uba Sani

Ko da yake bai bayyana cikakken dalilin yin furucinsa ba, kalamansa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zarge shi da amfani da ƴan sanda don tsoratar da magoya bayansa.

El-Rufai ya yi wannan zargi ne makon da ya gabata bayan da aka kama ɗaya daga cikin na kusa da shi, Jafaru Sani, wanda ya taɓa zama kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa a lokacin gwamnatinsa.

Wane martani gwamna Uba Sani ya yi?

A wata magana da ake ganin tamkar martani ne ga zargin El-Rufai, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa:

“Abin da ke gabana shi ne yin aiki domin al’ummar jihar Kaduna da suka zaɓe ni. Ba zan ɓata lokaci wajen ƙananan maganganu marasa amfani da ba za su kawo ci gaba ba."

Gwamna Uba Sani ya kuma bayyana ci gaban da gwamnatinsa ta samu cikin watanni 22 da suka gabata, musamman a fannonin noma, ilimi, da tsaro a yankunan da suka sha fama da matsalolin rashin tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mahaddacin Kur'anin da suka sace a Katsina? An gano gaskiya

"Mun samu gagarumar nasara wajen magance matsalolin tsaro a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa."
"Kasuwar shanu ta Birnin Gwari, wacce aka rufe fiye da shekara 10 saboda matsalar tsaro, an sake buɗe ta a watan Nuwamban da ya gabata, kuma harkokin kasuwanci suna bunƙasa.”

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani na jin daɗin tallata nasarorinsa

Gwamnan ya kuma nuna godiyarsa ga masu faɗa a ji a kafafen sada zumuntan bisa tallafawa gwamnatinsa wajen yaɗa nasarorin da take samu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Ina matuƙar godiya da yadda kuke haskaka nasarorin gwamnatina. Za mu ci gaba da tallafa muku domin ƙara yaɗa ayyukan alheri na gwamnatinmu."

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba ya samu goyon baya a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi (ALGON), reshen jihar Kaduna ta bayyana aniyarta na goyon bayan Gwamna Uba Sani a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Matsalar Obasanjo da Atiku: Kalaman El-Rufai sun ba da mamaki kan rigimarsu a baya

Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta tabbatar da cewa a zaɓen shekarar 2027, Gwamna Uba Sani ya samu ƙuri'u masu yawa don yin tazarce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel