El Rufai Ya Gamu da Matsala bayan Komawa SDP, Ƴan Kasuwa da Mata Sun Yi Masa Bore

El Rufai Ya Gamu da Matsala bayan Komawa SDP, Ƴan Kasuwa da Mata Sun Yi Masa Bore

  • 'Yan kasuwa da ƙungiyoyin mata sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna, suna nuna goyon baya ga Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Tinubu
  • Masu zanga-zangar sun ce sun fuskanci wahalhalu a mulkin Nasir El-Rufa’i, inda aka rusa kasuwanni, tare da jefa ’yan kasuwa cikin wahala
  • Sun gudanar da wannan zanga-zangar ne 'yan kwanaki bayan ficewar El-Rufai daga APC zuwa SDP, inda suka ce ba za su yarda a yaudare su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna – Daruruwan ’yan kasuwa da ƙungiyoyin mata sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kaduna, suna nuna goyon baya ga Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Tinubu.

Masu zanga-zangar sun ce sun fuskanci wahalhalu a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, tare da kira ga al’ummar jihar da kada su bari a yaudare su.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

Masu zanga zangar sun zargi El-Rufai da jefa 'yan kasuwa a cikin wahala a lokacin da yake gwamnan Kaduna
'Yan kasuwa da mata sun fita zanga-zangar lumana a Kaduna bayan sauya shekar El-Rufai. Hoto: @KadunaNews247
Asali: Twitter

'Yan kasuwa sun zargi El-Rufai da rusa shaguna

Sun yi ikirarin cewa, a cikin shekaru takwas na mulkin El-Rufa’i, an kwace ko an rusa daruruwan shaguna, abin da ya jefa ’yan kasuwa a talauci, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jigo a kungiyar ’yan kasuwa, Daniel Audu Maigari, ya ce sun shafe sama da shekaru 40 suna kasuwanci amma ba su taɓa fuskantar matsala irin ta mulkin da ya gabata ba.

“An rasa rayuka da dukiyoyi saboda tsare-tsaren tsohon gwamnan. Mun fito yau domin mu nuna rashin amincewarmu da duk abin da zai mayar da Kaduna baya."

- Daniel Audu Maigari.

Ya ƙara da cewa Gwamna Uba Sani ya fara magance matsalolin da suka faru a baya, kuma yana aiwatar da shirye-shiryen inganta kasuwanci a jihar.

Jigon ya nuna cewa:

“A baya ba mu jin tasirin shugabanci a kasuwannin Kaduna, amma yanzu muna amfana da shirye-shirye da manufofin Uba Sani da ke kawo ma ci gaba."

Kara karanta wannan

Siyasa mugun wasa: El Rufa'i na fatan Atiku da Obi su hade da shi a SDP

"Uba Sani ba zai cutar da mu ba" - Mai Gwanjo

Shugaban ƙungiyar ’yan kasuwa, Alhaji Daiyabu Ismail Mai Gwanjo, ya ce a madadin shugabansu, Alhaji Abdurrahman Mohammed, sun taru ne don nuna cikakken goyon baya ga Gwamna Uba Sani.

Ya ce ’yan kasuwa ba za su manta da wahalhalun da suka sha a lokacin tsohon gwamnan ba, inda aka rusa shagunansu, wanda ya sa da dama daga cikinsu suka samu karayar arziki.

“Amma tun da Allah ya kawo mana Gwamna Uba Sani, ya bayyana cewa ba zai cutar da ’yan kasuwa ba, domin kasashe masu ci gaba suna kare kasuwanci,” in ji Mai Gwanjo.

Ya ce a lokacin tsohuwar gwamnati, kimanin kasuwanni 36 aka rushe, amma har yanzu ba a sake gina su ba, lamarin da ke nuna wata manufa ta ɓoye da ta sa aka yi rusau din.

Kara karanta wannan

Kalaman El Rufa'i sun tada ƙura, ƴan sanda sun yi magana kan zargin 'sace kwamishina'

Saboda haka, Mai Gwanzo ya roki gwamnatin Kaduna, yana mai cewa:

“Muna kira ga Gwamna Uba Sani da ya duba batun, domin yana da tausayi kuma yana fahimtar halin da muke ciki."

Mata sun nuna goyon baya ga APC, Uba Sani

'Yan kasuwa da mata sun fita zanga-zanga a Kaduna
Yadda mata da 'yan kasuwa suka fita zanga-zanga a Kaduna bayan sauya shekar El-Rufai. Hoto: @KadunaNews247
Asali: Twitter

Hajiya Hadiza Abdulaziz, shugabar mata ta ƙungiyar 'yan kasuwa, ta ce sun taru ne domin nuna goyon baya ga APC da Gwamna Uba Sani da ke taimaka wa ’yan kasuwa.

“Yawancin mata sun rasa shaguna a baya, amma yanzu godiya ta tabbata ga Allah, an dawo da su, kuma ba za a sake kwacewa ba,” inji Hajiya Hadiza.

Ta bayyana farin ciki cewa waɗanda suka hana mata ci gaba a baya sun bar jam’iyyar da gwamnati, tana mai cewa Uba Sani zai taimakawa 'yan kasuwa da jari yanzu.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki suna ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce, suna rera waƙoƙin goyon baya ga Shugaba Tinubu, Uba Sani da jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tsofaffin ministocin Buhari 10 da manyan ƙusoshi na shirin bin El Rufai zuwa SDP

El-Rufai ya fice daga APC, ya koma SDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP domin ci gaba da siyasa.

Wasikar murabus dinsa da ke yawo a kafafen sada zumunta ta nuna cewa ya aike da takardar ficewa daga APC zuwa mazabarsa a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel