Hukumar KASUPDA tayi wasu rushe-rushe a Garin Kaduna

Hukumar KASUPDA tayi wasu rushe-rushe a Garin Kaduna

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa Hukumar nan ta KASUPDA da ke kula da sha’anin gine-gine a Jihar Kaduna tayi wasu rushe-rushe a cikin Garin na Kaduna cikin ‘yan kwanakin nan.

Hukumar KASUPDA tayi wasu rushe-rushe a Garin Kaduna
KASUPDA ta rusa shaguna da dama a cikin Kaduna
Asali: UGC

Hukumar ta KASUPDA ta rusa shaguna 80 a Unguwar Malali da ke cikin Garin na Kaduna kamar yadda Daily Trust ta rahoto. Nuhu Garba wanda shi ne Jami’in da ke magana da yawun Hukumar ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan.

Babban Jami’in na Hukumar ta Kaduna State Urban Planning and Development Agency ya fadawa Jaridar Daily Trust cewa shafunan da aka rusa a kan titin Liberia road da ke cikin Unguwar Malali sun sabawa ka’ida da dokokin kasa.

KU KARANTA: Mazauna birnin Abuja sun firgita yayin da aka yi girgizan kasa da daddare

A cewar Hukumar, an gargadi masu wadannan shaguna su tashi amma su ka yi mursisi su ka cigaba da zaman su a kan titi. Wadannan shaguna da aka rusa su na bayan wata Makarantar Gwamnati ta koyon aiki ne da ke Unguwar ta Malali.

Jami’in da yayi magana a madadin Hukumar, ya bayyana cewa an sanar masu shagunan da su ka tokare kan titi cewa za ayi rushe-rushe tun kusan wata guda kafin ayi wannan aiki. Gwamnati dai ba ta son ganin gini ya kare hanyar ruwa ko wuta ko titi.

Kwanaki idan ba ku manta ba Gwamnatin Jihar Kaduna ta rusa gidan wani 'Dan adawar Gwamna bisa zargin cewa ba a biya Gwamnati wasu kudi da su ka dace ba. Duk da Kotu ta dakatar da rusa wannan gida, wannan bai hana Gwamnati take umarnin Kotu ta rusa ginin ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng