Tirkashi: Dangote Ya Tsallake Najeriya, Ya Shigo da Ɗanyen Mai daga Ƙasar Waje
- Matatar Dangote ta sayi ganga 950,000 na danyen man Ceiba daga Equatorial Guinea, wanda zai iso matatar tsakanin 12 zuwa 13 ga watan Afrilu
- Rahotanni sun nuna cewa NNPC ta aika da jiragen ruwai dauke da danyen mai zuwa matatar Dangote domin ci gaba da sarrafawa a Najeriya
- Aliko Dangote ya bayyana cewa matatar tana shirin kai cikakken ƙarfin tace mai a watan Maris, amma ƙarancin danyen mai na iya hana hakan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Matatar man fetur ta Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana ta sayi jirgin danyen mai na farko daga Equatorial Guinea, nau’in Ceiba.
Rahotanni na nuna cewa Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya aika da sababbin jiragen danyen mai zuwa matatar Dangote domin ci gaba da sarrafawa.

Asali: UGC
Dangote ya sayo danyen mai a Equatorial Guinea
Majiyoyi sun bayyana cewa Dangote ya sayi gangar danyen mai 950,000 daga kamfanin BP na Equatorial Guinea, wanda zai sauke a ranar 12 zuwa 13 ga Afrilu, inji rahoton Argus Media.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce Equatorial Guinea ta fi fitar da man Ceiba zuwa zuwa China, inda take aikawa kasar kimanin ganga 18,000 a kowace rana.
Sannan an bayyana cewa kamfanin BP zai kuma tura man Ceiba da aka loda a Fabrairu da Maris zuwa Zhanjiang, da ke China.
Dalilin Dangote na sayo mai daga kasashen waje
Masana kasuwar mai sun bayyana cewa siyan Ceiba na daga cikin dabarun matatar Dangote na samun danyen mai daga wurare daban-daban.
A watan da ya gabata, matatar Dangote ta sayi nau’in danyen mai na Algeria, Saharan Blend, daga kamfanin Glencore, wanda zai iso gareta tsakanin 15 da 20 ga Maris.
Majiyoyi sun ce Dangote na kokarin sayo danyen mai a farashi mai sauƙi daga waje, yayin da kasuwannin Turai ke fuskantar raguwar buƙata saboda wadatar mai mai rahusa daga wasu ƙasashe.
Ana samun raguwar bukatar danyen man Najeriya
Yawaitar wadatar danyen mai daga Kazakhstan, Amurka, da yankin Mediterranean yana rage buƙatar danyen man Najeriya a kasuwannin Turai.
Bugu da ƙari, wasu matatun mai a Turai za su shiga gyaran matatunsu a watan Afrilu, wanda ke ƙara rage buƙatar danyen mai daga Najeriya.
Kamfanin NNPC ya tabbatar da cewa yana tattaunawa da matatar Dangote kan ci gaba da tsarin sayen danyen mai da Naira, inda farashin ke a dalar Amurka amma biya ke a naira.
Dangote zai sayo kaso 50% na danyen mai daga waje

Asali: UGC
Jaridar Punch ta rahoto cewa, masana na hasashen canjin ka’idojin cinikin danyen mai da Naira ka iya sa Dangote ƙara sayen danyen mai daga ƙasashen waje.
Masana masana’antar mai sun bayyana cewa matatar Dangote na shirin sayo aƙalla kashi 50 cikin 100 na danyen mainta daga ƙasashen waje.
Aliko Dangote ya bayyana cewa matatarsa tana shirin kai cikakken ƙarfin sarrafa mai a watan Maris, amma ƙarancin danyen mai na iya hana cimma wannan buri.
Dangote ya kara sauke farashin mai daga N825
A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta saukar da farashin man fetur daga N825 zuwa N815, wanda ya sa ‘yan kasuwa suka fara siye kai tsaye daga matatar.
Farashin shigo da fetur daga kasashen waje ya ragu zuwa N774.72 kan kowace lita, wanda zai iya haifar da saukar farashin a gidajen mai.
Asali: Legit.ng