"Masu Yin Don Allah": Farfesa Pantami Ya Fadi Yadda Ya Saba Tsarin da Ake Yi a Gwamnati

"Masu Yin Don Allah": Farfesa Pantami Ya Fadi Yadda Ya Saba Tsarin da Ake Yi a Gwamnati

  • Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa bai tafi da motar gwamnati ba bayan ya bar ofis
  • Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa ya ƙi tafiya da motocin ministan ne saboda bai yarda da halascin yin hakan ba
  • Farfesa Pantami ya nuna cewa dukkanin motocin da aka ba shi, sai da ya mayar da su a ma'aikatar sadarwa da tatalin zamani

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ministan sadarwa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi magana kan motocin da ya yi amfani da su.

Farfesa Pantami ya bayyana cewa bai ci gaba da amfani da mota ko guda ɗaya ba daga cikin motocin da aka ba shi na ofis a lokacin da yake minista.

Farfesa Pantami ya ce bai rike motocin gwamnati ba
Farfesa Pantami ya ce ya maida motocin gwamnati bayan ya bar ofis Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Farfesa Pantami ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo na wajen tafsir na watan Ramadan, wanda wani mai amfani da @el_uthmaan ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Albarkacin azumi: Yadda almajirai suka yi cudanya da gwamnan Nasarawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Pantami ya maida motocin gwamnati

Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa ya tattara dukkanin motocin da aka ba shi ya mayar da su ofis bayan ya sauka daga muƙamin minista.

Ya bayyana cewa ya ƙi yarda ya ci gaba da amfani da motocin ne saboda bai yarda cewa yin amfani da su halal ba ne.

Tsohon ministan ya nuna cewa duk da haka aka saba ana yi, idan mutum ya sauka daga kan kujera ya tafi da motocin hukuma, shi ko kaɗan bai gamsu da ya yi hakan ba.

Ya ce tun da tsarin ba a rubuce yake ba, bai yarda ya bi sahu shi ma ya tafi da motocin su zama na sa ba.

Meyasa Pantami ya ƙi yarda da tsarin?

Farfesa Pantami ya bayyana cewa ya gamsu da tsarin a yi ciniki mutum ya biya, amma bai yarda da kawai don ya gama ofis ya tafi da kadarorin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Rashawa: Obasanjo ya nemi kwacewa Buhari zani a kasuwa, Malami ya kare kansa

Ya nuna cewa ya ƙi yarda da hakan ne saboda ya san akwai ayoyin Al-Ƙur'ani da suka haramta, sannan a matsayinsa na mai addini, idan ya yi hakan, to za a yi ƙoƙarin tozarta addininsa.

"Ranar da na kammala aiki na a 29 ga watan Mayun 2023, sai da na cewa CSO ya ɗauki dukkan motocin gwamnati a gida na, guda shida ne ya mayar da su ma'aikata ya ba su."
"Na ce masa ya je ya ba su su yi yarjejeniya kowace mota da lambarta, da lambar injinta, su sanya hannu cewa babu motar hukuma ɗaya a hannuna."
"Abokaina suna cewa su sun ɗauka, na ce ni wallahi ba zan ɗauka ba ban yarda halal ba ne."

- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami

Ana son Pantami ya fito takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa an fara ƙoƙarin ganin tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya fito takara.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Ƙungiyar mai zaman kanta mai suna ‘Gombe State Promoters Forum in Broadcasting Media’ ta roƙi sanannen malamin addinin Musulunci ya fito takara a zaɓen 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel