Sojoji Sun Tumurmusa Ƴan Bindiga, Sama da 70 Sun Baƙunci Lahira a Watan Azumi

Sojoji Sun Tumurmusa Ƴan Bindiga, Sama da 70 Sun Baƙunci Lahira a Watan Azumi

  • Gwarazan dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarori masu dumbin yawa kan ƴan tada kayar baya a tsakanin ranar 5 zuwa 13 ga watan Maris, 2025
  • Mai magana da yawun hedkwatar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ya ce sojoji sun kashe ƴan bindiga 74, sun ceto mutane 61 a mako guda
  • Janar Markus Kangye ya bayyana cewa wasu ƴan ta'adda 143 sun miƙa wuya tare da ajiye makamansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Dakarun Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 74, tare da cafke wasu miyagu 130 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a kasar nan.

Gwarazan sojojin sun kuma kara da ƴan bindiga da sauran nau'ikan ƴan ta'adda kuma sun kuɓutar da mutane 61 da aka yi garkuwa da su duk a mako guda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga, sun hallaka miyagu a Zamfara

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 74, sun kama asu a mako 1 Hoto: @nigeriaarmy
Asali: Facebook

Babbar hedkwatar rundunar sojoji watau DHQ ce ta bayyana hakan, ta ce dakarun sun samu wannan nasara a makon da muke bankwana da shi, Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar DHQ, sojoji sun samu galaba mai tarin yawa tare da ƙwato makamai a yaƙin da suke yi da ƴan tada ƙayar baya daga ranar 5 zuwa 13 ga watan Maris, 2025.

Daraktan yada labaran na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a cikin rahoton mako-mako na ayyukan tsaro da aka fitar ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce dakarun sojojin sun kwato mugayen makamai da kayan aikin da ƴan binidga ke amfani da su a samame daban-daban a faɗin ƙasar nan.

Makaman da sojoji suka kwato a mako 1

A cewarsa, sojojin Najeriya sun yi aikin ne tare da hadin gwiwar ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro (ONSA) da kuma sojojin hadin gwiwa.

Kara karanta wannan

Katsina: Sojojin sama sun ragargaji 'yan bindiga, sun hallaka miyagu masu yawa

Dakarun tsaron sun kwato makamai 71, wanda suka hada da, bindigogi AK-47 guda 32, bindigogi kirar gida 15, bindigogi irin na farauta 9 da sauransu.

Haka nan kuma sojojin sun kwato alburusai 1,202, ciki har da albursai masu nauyin 7.62 guda 1,133, da harsasan bindiga 69.

Yan ta'adda 143 sun miƙa wuya ga sojoji

Bugu da ƙari, kakakin DHQ, Kangye ya ce a mako da ya gabata, ƴan ta'adda 143 da suka haɗa da maza biyar, mata 66 da ƙananan yaransu 72 sun miƙa wuya ga sojoji a Arewa maso Gabas.

Ɗaya daga cikin kwamandojin ƴan ta'addan ya mika wuya tare da ajiye makamai da suka haɗa da bindigun AK-47 guda biyu da alburusai 33, rahoton Leadership.

Sojoji.
Sojojin sun samu nasarori kan yan tada kayar baya a Najeriya Hoto: @InfoDefenceNG
Asali: Facebook

Janar Kangye ya tabbatar da cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa bisa ka’idojin aiki da dokokin tsaro na kasa.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi rashin imani, sun tashi mutanen garuruwa 5 ana azumi

"Sojojin Najeriya za su ci gaba da kare kasar nan daga ‘yan ta’adda da masu tayar da zaune tsaye, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali," in ji shi.

Sojoji sun daƙile harin ƴan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar daƙile harin ƴan ta'adda a jihar Zamfara.

Wata majiya daga ɓangaren tsaro ta bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, dakarun soji da ƴan sa-kai sun yi gaggawar fuskantar ƴan bindigan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262