Sojoji Sun Yi Wa Ƴan Ta'adda Bazata, Sun Hallaka Rikakken Ɗan Bindiga a Zamfara
- Sojojin 'Operation Fansan Yanma' sun kashe 'yan ta'adda 12 a kauyen Maigora da ke Faskari, sun kwato babura da dama daga hannunsu
- Daga cikin wadanda aka kashe akwai wani shahararren shugaban 'yan bindiga mai suna Kachallah Dogo, wanda aka tabbatar da mutuwarsa
- An ce Dogo wani shugaban gungun ‘yan bindiga ne da aka kashe a artabun da dakarun suka yi da su a yankin
- Wannan na zuwa ne yayin wani hari na dabam inda dakarun tsaro suka cafke Lawali Malangaro, wanda ke taimaka wa Kachalla Dan Mai Kinni a Zamfara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Dakarun 'Operation Fansan Yanma' da ke sintiri a Maigora, karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, sun kashe ‘yan ta’adda 12..
Rahotanni daga majiyoyi sun ce 'yan bindigar sun mamaye garin da misalin karfe 12:30 na rana ranar Juma'a.

Asali: Twitter
An yi ajalin rikakken ɗan bindiga a Zamfara
Sai dai dakarun da ke kusa da yankin sun amsa kiran gaggawa, suka shiga artabu da 'yan ta'addan har suka tsere da gudu, cewar rahoton Zagazola Makama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta ruwaito muku cewa rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta dakile harin ramuwar gayyan ‘yan bindiga a Mada, karamar hukumar Gusau da ke jihar Zamfara.
Harin ya auku da safiyar ranar Laraba yayin da ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari domin daukar fansa kan samamen baya-bayan nan.
Sojojin 'Operation Fansan Yamma' tare da jami’an sa-kai na Askarawa suka dauki mataki cikin gaggawa, suka shiga fafatawa mai tsanani da ‘yan ta’addan.
An kashe wasu ƴan bindiga 5 a Zamfara
A harin farko, dakarun sun kashe 'yan bindiga biyar tare da kwace babura guda biyu daga hannunsu.
A wani samame na bin sawu, 'yan bindigar sun sake dawowa domin ramuwar gayya, amma sojoji suka fatattake su.
Dakarun suka bi su cikin duwatsu, inda suka harbe su da makamai, suka kashe karin guda bakwai.

Asali: Facebook
Matakin rundunar sojoji kan ƴan ta'adda
Daga baya, sojojin sun ci gaba da sintiri a yankin, inda suka kwato wasu babura guda bakwai daga hannun ‘yan ta’addan.
Rahoton bincike ya nuna cewa wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Malum ya samu raunin harbin bindiga.
Wata majiya ta tabbatar da cewa an binne akalla 'yan bindiga goma sha biyu a yammacin Juma’a, ciki har da Dogo.
Dogo wani shugaban gungun ‘yan bindiga ne da aka kashe a artabun da dakarun suka yi da su a yankin.
Jami’an tsaro sun ci gaba da kafa sansani a yankin domin hana sake dawowar ‘yan ta’adda ko wani hari.
Sojojin sama sun ragargaji ƴan bindiga da dama
Kun ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasara kan ƴan bindigan da ke kai hare-hare a jihar Katsina.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka
Rahotanni sun ce Sojojin rundunar Operation Fansan Yamma sun kai farmaki a kan maɓoyar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar.
An ce jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga 19, ciki har da wasu manyan jagororinsu guda biyu a yayin farmakin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng