Zargin Shugaban Majalisa da Neman Matar Aure Ya Dawo, Kwamiti Ya Kira Akpabio da Natasha
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za su gurfana a gaban kwamitin Ladabtarwa
- Akpabio da Natasha za su bayyana gaban kwamitin ne domin bayani kan zargin neman lalata da sanatar Kogi ta yi wa shugaban Majalisa
- Wannan dai na zuwa ne makonni bayan dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida, tare da hana ta albashi da alawus-alawus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar Dattawa ta hannun kwamitin ladabtarwa da ɗa'a, za ta fara bincike kan zargin shugaban Majalisa, Godswill Akpabio da neman latata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Akpabio, da sanata mai wakiltar Kogi Tsakiya, za su gurfana gaban Kwamitin Ladabtarwa domin bayani kan zargin cin zarafi da Natasha ta yi.

Asali: Twitter
Kwamitin majalisa ya kira Akpabio da Natasha
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Mataimakin Mai Ladabtarwa, Sanata Onyekachi Nwebonyi, a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na Channels TV ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Dukkan bangarorin da abin ya shafa za su bayyana gaban kwamitin, ciki har da shugaban majalisar dattawa. Za a saurari shaidarsu kuma za a ɗauki bayanansu, za kuma a saurari sauran sanatoci."
Wane zargi Natasha ta yi wa Akpabio?
A ranar 28 ga Fabrairu, Natasha ta bayyana cewa Akpabio ya nemi lalata da ita a watan Disamba 2023 lokacin da ita da mijinta suka kai masa ziyara a gidansa da ke Uyo, jihar Akwa Ibom.
Ta ce:
"A lokacin wannan ziyara, Shugaban Majalisar ya rike hannuna, ya zagaya da ni cikin gidansa, sannan ya yi kokarin yi min abin da bai dace ba, har a gaban mijina."
Sanatoci za su ba da shaida kan zargin
Sanata Nwebonyi ya zargi Natasha da kokarin karkatar da hankalin jama’a. Ya ce:
"A dokar shari’a, akwai abin da ake kira hujja a fili. Idan babu hujja a fili, to babu shari’a. A ranar da take cewa lamarin ya faru, akwai sanatoci da yawa a wurin.
"Ni ma ina daga cikin sanatocin da suka kasance a wurin, kuma zan bada shaidar abin da na gani."
Dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha
Idan ba ku manta ɗa Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida bisa laifin karya dokokinta.
Majalisar ta bayyana cewa dakatarwar ba ta ɗa alaƙa da zargin da take yi wa Akpabio, an ɗauki matakin ne kan hayaniyar ta tayar game da wurin zama.

Asali: Facebook
Yayin da ake ta kiraye-kirayen a yi wa sanatar adalci, Majalisar ta tabbatar da cewa za a gudanar da bincike kan zargin cin zarafin da ta yi wa Akpabio.
A halin yanzu, Akpabio da Natasha za su gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa domin jin ta bakin kowanensu kan zargin cin zarafi.
Sanatoci na goyon bayan Akpabio?
A wani rahoton, kun ji cewa sanatocin Najeriya sun kaɗa kuri'ar amincewa da shugabancin Sanata Godswill Akpabio a zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis.
Ƴan majalisar sun jaddada goyon bayansu ga Akpabio duk da zargin cin zarafin da abokiyar aikinsu daga jihar Kogi, Sanata Natasha take masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng