Mutuwa Mai Yankar Ƙauna: Tsohon Dan Majalisa Ya Rasu Kwanaki 7 kafin Bikin Karin Shekara

Mutuwa Mai Yankar Ƙauna: Tsohon Dan Majalisa Ya Rasu Kwanaki 7 kafin Bikin Karin Shekara

  • An tabbatar da rasuwar tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin jihar Oyo kuma babban jigo a jam'iyyar APC, Hon. Kehinde Subair
  • Tsohon ɗan Majalisar Dokokin ya riga mu gidan gaskiya ne a Birtaniya ranar Juma'a, 13 ga watan Maris, mako guda kafin ya cika shekara 60
  • Sanata mai wakiltar Oyo ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Yunus Akintunde ya yi alhinin rashin tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo - Tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Kehinde Subair, ya riga mu gidan gaskiya ranar Juma'a, 14 ga watan Maris, 2025.

Sanata Yunus Akintunde, mai wakiltar jihar Oyo ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya, ne ya tabbatar da rasuwarsa a ranar Juma’a.

Kehinde Subair.
Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Kehinde Subair, ya rasu Hoto: Joseph Olayinka
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta kawo, mai taimakawa Sanata Yunus kan harkokin yaɗa labarai, Kunle Olatunji shi ne ya sanar da rasuwar a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Sanatan Yunus Akintunde ya bayyana mutuwar Subair a matsayin babban rashi ga jam’iyyar APC, jihar Oyo da kuma Najeriya baki ɗaya.

Tsohon shugaba a Majalisa ya rasu

Sanata Akintunde ya ce:

"Na samu labarin rasuwar Hon. Kehinde Subair cikin baƙin ciki da jimami, ya kasance babban abokina ne kuma babban jigo a harkokin siyasar jihar Oyo."
"Rasuwarsa kwatsam ba zato ba tsammani ta bar babban gibi da zai yi wahala a iya cike shi. Za a yi kewar jagorancinsa mai fa’ida da kuma halayensa na son zaman lafiya."
"Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalansa, al’ummar jihar Oyo da ya yi wa hidima da kuma daukacin ‘yan jam’iyyar APC."

Sanatan Oyo ya miƙa saƙon ta'aziyya

Sanatan ya kara da cewa marigayin ya ba da gudummuwa sosai a ƙoƙarin farfaɗo da jam'iyyar APC ta jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

"Subair ya taka rawar gani sosai a shirin gyaran jam’iyyarmu ta APC a ‘yan shekarun nan. Halayensa na kirki da kyautatawa mutane za su kasance abin tunawa."

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu sun hada kai, ana shirin samawa matasa miliyan 5 aiki

"Allah Ya jikansa ya gafarta masa, ya ba mu haƙuri da juriyar wannan babban rashi," in ji shi.
Kehinde Subair.
Allah ya yi wa tsohon ɗan Majalisa rasuwa. a Birtaniya Hoto: Joseph Olayinka
Asali: Facebook

Taƙaitaccen tarihin rayuwar marigayin

Kehinde Subair ya riƙe muƙamin mamba a Majalisar Dokokin Jihar Oyo har sau biyu a tarihin siyasarsa.

Ya kuma zama Shugaban Masu Rinjaye a majalisar a lokacin zango na biyu na mulkin tsohon Gwamna Abiola Ajimobi.

Tsohon ɗan Majalisar ya rasu ne a ƙasar Birtaniya, kwana bakwai kafin bikin cika shekaru 60 da haihuwarsa a duniya.

Tsohon minista a Najeriya ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon karamin ministan harkokin kasashen waje, Dubem Onyia ya kwanta dama yana da shekaru 73 a duniya.

Majiyoyi daga iyalansa da abokan aikinsa sun tabbatar da rasuwarsa a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 10 ga watan Maris, 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng