Kogi: Rikici Ya Tsananta a SDP Kwanaki da Komawar El Rufai, Jam'iyyar Ta Dare 2

Kogi: Rikici Ya Tsananta a SDP Kwanaki da Komawar El Rufai, Jam'iyyar Ta Dare 2

  • Jam’iyyar SDP reshen jihar Kogi ta fada cikin rikici bayan wani sabon tsagi ya gudanar da zabe tare da rantsar da sababbin shugabanni a Lokoja
  • An ce sabon kwamitin mai mambobi 12 ya samu amincewar wakilai 3,890 daga kananan hukumomi 21, kuma jami'an INEC suka sa ido a zaben
  • Sai dai, tsagin Moses Peter Oricha ya yi watsi da zaben, yana mai cewa ba bisa ka’ida aka gudanar da shi ba kuma ba za su yarda da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Jam’iyyar SDP reshen jihar Kogi ta fada cikin rikici bayan wani sabon tsagi ya kaddamar da sababbin shugabanni a Lokoja, a ranar Laraba.

Taron ya gudana ne a sakatariyar jam’iyyar, inda tsohon jigon APC, Hon. Ahmed Attah, ya zama sabon shugaban SDP na jiha, yayin da Alhaji Idris Sofada ya zama sakatare.

Kara karanta wannan

"Jonathan ya yi bankwana da siyasa," PDP ta magantu kan fito da shi takara

An samu sabon tsagin shugabanci a jam'iyyar SDP reshen jihar Kogi
Rikicin shugabanci ya barke a SDP reshen Kogi da aka samu sabon tsagi. Hoto: @Motisuccess
Asali: UGC

An samu sabon shugaban SDP a jihar Kogi

Sabon kwamitin gudanarwar mai mambobi 12 ya samu amincewa daga wakilai 3,890 na kananan hukumomi 21 na jihar Kogi, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya kuma nuna cewa akwai jami'an sa ido daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a lokacin da aka kafa tsagin jam'iyyar.

A jawabinsa na bayan rantsuwa, Hon. Ahmed Attah ya yi alkawarin gudanar da shugabanci na gaskiya tare da yi wa dukkanin 'ya'yan jam'iyyar adalci.

Sabon shugaban ya kuma yi alkawarin inganta tsarin jam’iyyar SDP domin ba ta damar lashe dukkanin zabukan da ke tafe.

Kogi: Jam'iyyar SDP ta dare gida biyu

Ya jinjinawa INEC, kwamitin shirya taron, da jami’an tsaro bisa kokarinsu na tabbatar da taron ya kammala cikin aminci ba tare da wata matsala ba.

Jaridar Tribune ta rahoto Hon. Ahmed Attah ya bayyana cewa:

“Wannan mataki ya sanya SDP ta zama jam’iyyar da za a fafata da ita kuma ta samu nasara a zaben gwamnan 2028.”

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a SDP bayan El Rufa'i ya koma cikin jam'iyyar

Sai dai, wani tsagin jam'iyyar karkashin jagorancin Moses Peter Oricha ta yi watsi da taron da ya samar da shugabancin Hon. Ahmed Attah.

Tsagin Moses Peter Oricha ya nuna cewa an gudanar da wancan taron ba bisa ka'ida ba, don haka ta nemi 'yan jam'iyyar su yi watsi da tsagin.

Tsagin Moses Oricha sun yi watsi da na Attah

Tsagin Moses Oricha sun yi watsi da tsagin Hon. Attah, lamarin da ya haddasa rikici a SDP, reshen Kogi
Shehu Musa Gabam, shugaban jam'iyyar SDP na kasa. Hoto: @Motisuccess
Asali: Twitter

Moses Oricha, wanda wa’adin mulkinsa zai kare a watan Afrilun 2026, ya zargi masu shirya taron da saba doka da kuma kin bin tsarin da ya dace.

Shugaban tsagin jam'iyyar ya ce:

“Na samu labarin cewa wasu mutane da ke ikirarin cewa ‘ya’yan SDP ne sun gudanar da taron zaben shugabanni. Wannan abin dariya ne domin an yi shi ba bisa doka ba."

Ya kara da cewa:

“Wadannan mutane babu sunansu a rajistar jam'iyyarmu, kuma wasu ne suka dauki nauyinsu domin tayar da hargitsi a jam’iyyar.”

Moses Oricha ya bukaci jama’a, hukumomin tsaro da INEC da su yi watsi da sabon zaben, yana mai cewa an shirya shi ne don tarwatsa SDP.

Kara karanta wannan

SDP: An zargi gwamnan APC da neman marin shugaban jam'iyyar El Rufa'i

Nasir El-Rufai ya koma jam'iyyar SDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP.

Wata wasika da ta karade kafafen sada zumunta ta nuna El-Rufai ya aike da takardar ficewarsa daga APC ga shugabancin jam’iyyar a mazabarsa da ke Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel