Tirkashi: Kwastam Ta Kama Dala Miliyan 1.1 da Aka Shigo da Su Kano daga Saudiyya
- Hukumar Kwastam ta kama dala $1.1 miliyan da Riyal 135,900 da ba a tantance su ba a filin jiragen sama na Mallam Aminu Kano, a jihar Kano
- An gano kudaden a cikin fakitin dabino yayin binciken wani fasinja da ya sauka daga jirgin Saudiyya mai lamba SV401 da ya taso daga Saudiyya
- Bayan gurfanar da wanda ake zargi, an kwace kudaden tare da mika su ga gwamnatin tarayya bisa tanadin dokar hana safarar kudade
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta ce jami’anta sun kama dalar Amurka $1.1 miliyan da Riyal 135,900 na Saudiyya a jihar Kano.
Hukumar hana fasa kwaurin ta ce an kama kudaden, wadanda ba a tantance su ba, a filin jiragen saman Mallam Aminu Kano, da ke jihar.

Asali: Twitter
An gano kudin a cikin jakunkunan dabino
A cikin wata sanarwa, kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada, ya bayyana cewa an boye wadannan makudan kudade a jakunkunan dabino, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maiwada ya ce an gano kudaden ne yayin binciken kayan wani fasinja da ya sauka daga jirgin Saudi Airline mai lamba SV401 da ya taso daga kasar Saudiyya.
Bayan an gurfanar da shi a gaban kotu, an samu mai kayan da laifi, kuma an umurce shi da ya mika kudaden da ba a tantance ba ga gwamnatin tarayya.
Kotu ta kwace dalolin da aka kama a Kano
Kakakin hukumar NCS, ya bayyana cewa:
“A bisa ka’ida, an mika wanda ake zargi da kudaden da aka kama ga hukumar EFCC domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin doka.
“Daga bisani, kotu ta yanke hukunci tare da umurtar a kwace kudaden da aka kama, bisa tanadin dokar hana safarar kudade ta 2022.”
Maiwada ya bayyana cewa wannan kame yana nuna kokarin hukumar kwastam na tabbatar da bin dokokin hada-hadar kudi da kuma dakile safarar kudade.
Ya bukaci matafiya da su bi dokokin hada-hadar kudi na Najeriya, tare da bayyana duk wani kudi ko kayan da darajarsu ta zarce iyakar da aka amince da ita.
“Rashin bin wadannan dokoki laifi ne a Najeriya, kuma yana janyo hukunci mai tsanani. Don haka, ana bukatar jama’a su kiyaye don gujewa fuskantar matsalolin shari’a,” in ji Maiwada.
Kwastam ta jajirce wajen hana fasa kwauri

Asali: Twitter
Ya kara da cewa, hukumar kwastam karkashin jagorancin kwamandan babban darakta, Adewale Adeniyi, tana da cikakken shiri na yaki da fasa-kwauri da hada-hadar haramtattun kudi.
Jaridar The Cable ta rahoto Maiwada ya ce:
“A karkashin wannan shugaba, hukumar kwastam za ta ci gaba da kokarinta wajen dakile manyan laifuffuka da suka shafi shige da fice a iyakokin kasar.”
Ya ce wannan kame na baya-bayan nan ya sake tabbatar da jajircewar hukumar wajen kare tattalin arzikin kasa da kuma tabbatar da bin dokokin hada-hadar kudi.

Kara karanta wannan
'Sun koma barayi': Ana zargin jami'an tsaron da gwamna ya kafa suna satar dabbobi
Hukumar ta bukaci dukkan matafiya da su guji safarar kudi ba bisa ka’ida ba, domin irin wadannan matakai na hana shige-da-ficen kudade ta haramtacciyar hanya.
Kwastam ta kama motocin Naira biliyan 5.64
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar kwastam ta Najeriya ta ce ta kama motoci 397 da kudinsu ya kai Naira biliyan 5.64 a shekarar 2024.
Hukumar ta kuma cafke magungunan jabu da darajarsu ta kai Naira biliyan 3.04, tare da buhunan shinkafa 183,527 domin kare tattalin arzikin kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng