Kwastam ta kama zunzurutun kudi har miliyan $8 a filin jirgin sama

Kwastam ta kama zunzurutun kudi har miliyan $8 a filin jirgin sama

Hukumar kwastam ta kasa ta kama wasu makuden kudade a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Hameed Ali, shugaban hukumar ta kasa, ya sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da aka yi a Abuja a ranar Talata. Ya ce an kama wadannan makuden kudaden ne a wata mota a filin jirgin yayin da ake yunkurin zuba su a jirgin saman.

Shugaban hukumar kwastam din ba ta bada bayanin jirgin ba amma ta bayyana cewa motar da aka kama kudin a ciki mallakin Nigerian Aviation Handling Company (NAHCO).

Kwastam ta kama zunzurutun kudi har miliyan $8 a filin jirgin sama
Kwastam ta kama zunzurutun kudi har miliyan $8 a filin jirgin sama
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya aika wa Nanono takardar neman ya kare kansa a kan wata harkallar takin noma

Ali ya ce wanda ake zargin matukin motar ne kuma ma'aikacin NAHCO. An kama shi ne sakamakon zargin da ake masa na almundahanar kudade, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ce an nade makuden kudaden ne a ambulan mai ruwan kasa tare da sunayen wadanda za a ba kudin.

"Daga rana da muka kwace kudaden, babu bankin da suka fito suka ce nasu ne. Amma kuma bincikenmu zai bankado mamallakan kudin," Ali ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel