Zargin Lalata: Majalisar Dattawa Ta Bayyana Matsayinta kan Shugabancin Akpabio

Zargin Lalata: Majalisar Dattawa Ta Bayyana Matsayinta kan Shugabancin Akpabio

  • Majalisar dattawan Najeriya ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da shugabancin Sanata Godswill Akpabio a ranar Alhamis, 13 ga watan Maris 2025
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da ƙudirin neman amincewa da shugabancin Akpabio
  • Bamidele ya bayyana cewa majalisar ba za ta bari wani abu ya riƙa ɗauke mata hankali kan dambarwar dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta bayyana matsayarta kan shugabancin Sanata Godwill Akpabio.

Majalisar dattawan ta kaɗa ƙuri’ar goyon baya da amincewa da shugabancin shugabanta, Sanata Godswill Akpabio.

Majalisar dattawa ta amince da shugabancin Akpabio
Majalisar dattawa ta kada kuri'ar amincewa da shugabancin Akpabio Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta amince da shugabancin Akpabio

Jaridar The Punch ta rahoto cewa sanatocin sun kaɗa ƙuri’ar goyon bayan ne ga Akpabio a zaman majalisar na ranar Alhamis, 13 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙuri'ar ta biyo bayan ƙudirin da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele (Ekiti ta Tsakiya), ya gabatar, wanda mataimakin shugaban marasa rinjaye, Olalere Oyewumi (Osun ta Yamma), ya mara masa baya.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta kai karar Akpabio ga kungiyar 'yan majalisun duniya

A cikin muhawararsa, Bamidele ya ce majalisar dattawa ta yanke shawarar ƙin bari wani abu ya ɗauke mata hankali, musamman kan dambarwar da ta biyo bayan dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin ɗa’a.

Shugaban masu rinjayen ya ce daga yanzu majalisar za ta mayar da hankali kan aikinta na yin dokoki da sa ido kan harkokin gwamnati, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Sanata Opeyemi ya ƙara da cewa majalisar za ta bari ɓangaren shari’a ya yanke hukunci kan ƙararrakin da aka shigar kan batun dakatar da Sanata Natasha.

Sanata Natasha ta kai ƙarar Akpabio

Wannan mataki na majalisar dattawa ya biyo bayan jawabin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wacce aka dakatar na tsawon watanni shida ba tare da albashi ba, ta yi a taron majalisun ƙasashen duniya (IPU) da aka gudanar a birnin New York.

A wajen taron, Sanata Natasha ta yi iƙirarin cewa an dakatar da ita ne saboda ta yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ci zarafinta.

Kara karanta wannan

Akpabio: Sanatan Arewa ya goyi bayan Natasha kan zargin cin zarafi? An fede gaskiya

Sanata Natasha ta kuma shigar da ƙarar raina umarnin kotu a kan Akpabio da wasu mutane, bisa dakatarwar da aka yi mata daga majalisar.

Majalisar dattawa ta buƙaci ƴan Najeriya da ka da su bari wannan zargin ya ɗauke musu hankali, tana mai jaddada cewa lamarin yana gaban kotu.

Ta kuma bayyana cewa ba za ta tsoma baki a cikin lamarin ba wanda yake a gaban kotu.

Ƙungiyar SERAP ta ba Akpabio wa'adi

A wani labarin kuma, kun ji cewa SERAP ta yi magana kan dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Ƙungiyar ta buƙaci shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, da ya ɗauki matakin janye dakatarwar da aka yi wa sanatar ta Kogi ta Tsakiya.

SERAP ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ta tauye haƙƙinta na ƴancin fadar albarkacin baki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel