An Yi Zazzafan Martani ga Gwamnatin Tarayya kan Hutun Azumi a Makarantun Arewa

An Yi Zazzafan Martani ga Gwamnatin Tarayya kan Hutun Azumi a Makarantun Arewa

  • Ana cigaba da maganganu yayin da jihohi hudu suka ki amincewa da buɗe makarantu da ake nema su yi a lokacin azumi
  • Tsohon kwamishinan ilimi a jihar Bauchi ya ce jihohi ne ke da hurumin rufe wa ko buɗe makarantu, ba gwamnatin tarayya ba
  • Dr Aliyu Tilde ya jaddada cewa babu asarar ilimi da za a yi saboda hutun, duba da yadda ake yawan hutun Asabar da Lahadi a shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Jihohi hudu a Arewacin Najeriya sun ƙi amincewa da buɗe makarantu da aka rufe saboda azumi, duk da tattaunawar da gwamnatin tarayya ta fara yi da su.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jami’an gwamnati na kokarin tursasa buɗe makarantun, duk da cewa jihohin sun tabbatar babu wata asarar karatu da za a yi.

Kara karanta wannan

"Mun ba ku lokaci," An tura motocin buldoza, sun rusa gidajen mutane da azumi a Abuja

Gwamnoni
Wasu daga cikin gwamnonin da suka ba da hutun azumi. Hoto: Nasir Idris|Lawal Muazu Bauchi|Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tsohon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dr Aliyu Tilde ya wallafa a Facebook cewa jihohin Arewa ba za su bude makarantu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Aliyu Tilde ya bayyana cewa doka ta bai wa jihohi damar rufe wa ko buɗe makarantu ba tare da katsalandan daga gwamnati tarayya ba.

Martanin Dr Tilde ya biyo bayan wata magana ne da ministar ilimi ta yi a kan cewa za ta tattauna da jihohin Kano, Bauchi, Katsina da Kebbi domin ganin sun dakatar da hutun da suka bayar.

Martanin Dr Tilde ga ministar ilimi

A cewar Dr Tilde, ba daidai ba ne gwamnatin tarayya ta tilasta jihohi su buɗe makarantu yayin da suke da ‘yancin yin hukunci a kan harkar ilimi.

Tsohon kwamishinan ya fada wa ministar ilimi cewa:

“Ki je ki karanta doka. Ilimin firamare da sakandare na jihohi ne, kuma hurumin su ne buɗe wa ko rufe makarantu.”

Kara karanta wannan

SDP: An zargi gwamnan APC da neman marin shugaban jam'iyyar El Rufa'i

Haka zalika, ya yi mamakin yadda wasu jami’an gwamnati ke magana bisa son zuciya, inda ya ce jihohin da suka rufe makarantu sun tabbatar da cewa babu wata matsala da hakan zai haifar.

Korafi kan hutun ranakun Asabar da Lahadi

Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa akwai hutun da ake yawan yi a shekara, amma ba a tayar da hankali a kansu kamar na Ramadan ba.

Dr Tilde ya ce:

“Kamar yadda Farfesa Lugga ya ce, duk shekara ana rasa kwanaki 104 saboda hutun Asabar da Lahadi na Kirista, amma Musulmi ba su ce komai ba.”

Ya kara da cewa rashin adalci ne a rika sukar hutun Ramadan, yayin da ake ganin na wasu addinan a matsayin hakkinsu.

Gwamnoni
Tsohon kwamishinan ilimi a jihar Bauchi. Hoto: Dr Aliyu Tilde
Asali: Facebook

Kira da a rungumi hutun Ramadan a Arewa

Dr Tilde ya ce, a maimakon ce-ce-ku-ce, kamata ya yi jihohin Arewa su samar da tsarin da zai bai wa yaran Musulmi damar samun hutu a Ramadan.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamnatin tarayya ta shiga batun hutun azumi a makarantun Arewa

A cewarsa:

“Ina ga ya kamata a jihohin Arewa mafi rinjayen Musulmi a dinga ba yara hutu a Ramadan, sai su fanshi hakan a sauran kwanakin shekara.”

Gwamnatoci sun yi martani ga CAN

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jihohi sun yi martani ga kungiyar CAN na cewa a bude makarantu da aka rufe a azumi.

Gwamnatocin Kano, Bauchi da Kebbi sun yi martani ga kungiyar CAN da cewa ba gudu ba ja da baya a kan ba da hutu a watan Ramadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng