"Mun Ba Ku Lokaci," An Tura Motocin Buldoza Sun Rusa Gidajen Mutane da Azumi a Abuja
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya jagoranci rusau a yankin Gishiri da ke cikin babban birnin tarayya domin ci gaba da aikin titi
- Da yake zantawa da manema labarai a wurin, Wike ya ce sun bai wa mutane diyya da tayin sauya masu matsugunai amma suka ƙi karba
- Ya ce gwamnati ba ta da wani zaɓi face rusa gidajen mutane bayan an ba su kusan watanni uku su kwashe kayansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ba da umarnin rushe wasu gidaje da ke kan hanya a yankin Gishiri da ke ƙarƙashin yankin Katampe a Abuja.
Ministan ya tura motocin buldoza tare da jami'an tsaro su rusa gidajen ne domin ci gaba da aikin titin da ake ginawa a yankin.

Kara karanta wannan
Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa

Source: Facebook
Channels tv ta ce a ranar Talata, Wike ya jagoranci rusau ɗin da kansa, aka hango shi cikin fushi ya na jan kunne ga shugaban al’ummar yankin, yana mai cewa, “Mun ba ku lokaci.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka rusa gidajen mutane a Abuja
Wasu daga cikin mazauna yankin sun yi ƙoƙarin hana aikin rusau ɗin, ta hanyar rufe hanya don dakatar da motocin buldoza da ke rushe gidajensu.
Sai dai ’yan sanda da wasu jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su, domin ba wa jami’ai damar yin aikinsu.
Da yake hira da manema labarai, Ministan Abuja ya bayyana cewa gwamnati ta bai wa mazauna yankin diyya, amma sun ƙi karɓa, abin da ya sa ba ta da wata zaɓi illa rusa gidajen domin aikin titin.
Dalilin rusau da fa’idar titin Gishiri
Wike ya bayyana cewa gwamnati ta bai wa mutanen yankin lokaci na wata uku don su tashi kuma su kwashe kayansu daga wurin, amma suka yi kunnen ƙashi.
Ministan ya ce:
"Na ziyarci wannan wuri fiye da sau huɗu, kuma na yi magana da shugabannin al’umma da sarakunan yankin. Ya kamata su ba da haɗin kai domin aikin titin nan ya kammala a kan lokaci.”

Source: Twitter
Mista Wike ya ƙara da cewa babu wata gwamnati da za ta ƙyale mutane su hana aiwatar da ayyukan ci gaba, yana mai cewa:
“Mun ba su wata biyu zuwa uku don su shirya. Mun kuma ba su diyya tare da shirin sake musu matsuguni. Me kuma kuke so mu yi?”
An ƙaddamar da aikin titin Gishiri a watan Oktoba 2024, kuma ana sa ran zai kammala a watan Mayu 2025, a matsayin wani muhimmin aikin raya ƙasa a ƙarƙashin mulkin Bola Tinubu.
Wike ya ƙara rarrashin ƴan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa ministan Abuja ya ba ƴan Najeriya tabbacin cewa abubuwa za su kyau nan gaba a karkashin mulkin shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Nyesom Wike ya ce Tinubu ya na da kyakkyawar niyya ga ƴan Najeriya, domin manufofin da gwamnatinsa ta fito da su, an kawo su ne da nufin gyara ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

