Hajjin Bana: NAHCON Ta Sanya Lokacin Fara Jigilar Maniyyata Zuwa Saudiyya

Hajjin Bana: NAHCON Ta Sanya Lokacin Fara Jigilar Maniyyata Zuwa Saudiyya

  • Shirye-shiryen fara jigilar maniyyatan Najeriya domin zuwa aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki na ci gaba da kankama
  • Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ce tana shirin fara jigilar maniyyata a cikin watan Mayun 2025 zuwa ƙasar Saudiyya
  • Daraktan ayyuka na hukumar NAHCON ya bayyana cewa Saudiyya za ta buɗe sararin samaniyarta a ƙarshen watan Afrilun 2025
  • Hukumar NAHCON dai ta zaɓo kamfanonin jiragen sama guda huɗu waɗanda za su yi jigilar maniyyata zuwa Kasa mai tsarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da shirinta na fara jigilar alhazan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki don aikin Hajjin bana.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa tana shirin fara jigilar maniyyata zuwa Saudiyya a watan Mayun 2025.

NAHCON za ta fara jigilar maniyyata
Za a fara jigilar maniyyata a watan Mayu Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Facebook

Kwamishinan ayyuka na NAHCON, Anofiu Elegushi, ya bayyana hakan a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

2027: Yan adawa na shirin firgita Tinubu, ƙusa a PDP ya ce guguwar canji za ta tafi da APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anofiu Elegushi ya yi magana ne yayin sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar Alhazai tare da kamfanonin jiragen sama guda huɗu, FlyNas, Air Peace, Max Air, da Umza Air Limited, a birnin tarayya Abuja.

Yaushe NAHCON za ta fara jigilar maniyyata?

A cewar Anofiu Elegushi, Saudiyya za ta buɗe sararin samaniyarta domin karɓar Alhazai daga ranar 29 ga watan Afrilu, yayin da jirgin farko daga Najeriya zai tashi a ranar 6 ga watan Mayu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

“Bisa bayanan da muka samu daga hukumomin Saudiyya, muna fatan cewa za su buɗe sararin samaniyarsu a ranar 29 ga Afrilu domin karɓar Alhazai."
“Amma a Najeriya, muna fatan jirgin farko zai tashi ranar 6 ga watan Mayu, Insha Allah."

- Anofiu Elegushi

Ya ƙara da cewa hukumar NAHCON na aiki kafaɗa da kafaɗa da kamfanonin jiragen sama domin sauƙaƙa jigilar Alhazai 75,000 daga jihohi daban-daban na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

El Rufai ya girgiza siyasar Najeriya, manyan jiga jigan APC na shirin komawa SDP

Anofiu Elegushi ya kuma bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin kawar da amfani da dala wajen biyan kamfanonin jiragen sama kuɗaɗensu.

A madadin haka, an shirya biyan kamfanonin jiragen cikin kuɗinsu na gida.

“Zamanin kwashe dogon lokaci ana jira domin biyan kuɗi ya wuce."

- Anofiu Elegushi

Hukumar NAHCON na son walwalar Alhazai

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya tabbatar da cewa hukumar na da cikakken shiri domin kyautata walwalar Alhazan Najeriya.

Ya jaddada cewa jigilar Alhazai na ɗaya daga cikin muhimman shirye-shiryen aikin Hajji.

Ya kuma bayyana cewa an zaɓi kamfanonin jiragen saman ne bisa cancanta da ƙwarewa domin tabbatar da cewa ƙwararrun masu jigilar fasinjoji ne kawai za su ɗauki Alhazan Najeriya.

Gwamna Radda ya ba NAHCON shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ba hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) shawarwar kan ayyukanta.

Gwamna Radda ya buƙaci hukumar da ta ɗauki matakan da za su rage yawan ƙalubalen da Alhazai suke fuskanta a ƙasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani kan sauya shekar El Rufai, ta fadi shirin da take yi

Ya kuma buƙaci NAHCON da ta rage yawan kwanakin da Alhazai ke yi a Saudiyya domin su samu sauƙin kashe kuɗi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel