'Muna Cikin Tashin Hankali': Daruruwan Mata Sun Fita Zanga Zanga a Jihar Benuwai
- Mata a Jato Aka sun yi zanga-zanga don nuna bacin ransu kan hare-haren da ake kai wa manoma, suna bukatar kariya da tsaro daga gwamnati
- Mazauna yankin sun ce an dade ana kai musu hare-hare, inda mutane da yawa suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga gidajensu
- Matan sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kara tsaro, ta gudanar da bincike, tare da kawo agaji ga 'yan gudun hijira da ke cikin mawuyacin hali
- Gwamna Hyacinth Alia ya bukaci jama’a su kwantar da hankali, yana mai cewa ya dauki matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benuwai - Mata a garin Jato Aka da ke karamar hukumar Kwande a jihar Benuwai sun gudanar da zanga-zanga kan harin da ake kai wa manoma.

Kara karanta wannan
'Sun koma barayi': Ana zargin jami'an tsaron da gwamna ya kafa suna satar dabbobi
Shugaban al’umma, Lawrence Akerigba, ya ce matan sun fita zanga-zangar don nuna damuwa kan yawan kashe-kashen da ake yi wa jama’a a yankin.

Asali: Original
Daruruwan mata sun fita zanga zanga a Benuwai
An dade ana kai wa al’ummar Jato Aka hare-hare, wanda a cikin watan da ya gabata ya yi sanadin mutuwar manoma da dama, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar mazauna yankin, mutanen gundumar Turan sun yi kaura daga gidajensu sama da shekaru 17 saboda yawaitar rikice-rikice.
Da dama daga cikin matan da suka fito zanga-zanga, 'yan gudun hijira ne, inda suka yi da'ira a wuraren da aka kwashe sojoji da kasuwar Jato Aka.
Rahoton ya nuna cewa ana kallon karamar hukumar Kwande a matsayin tushen kabilar Tibi da ke a jihar Benue.
Mata sun nemi a kaiwa 'yan gudun hijira dauki
Matan sun yi wake-wake tare da daga ganyaye suna kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo dauki domin shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu
Sun bukaci a dakatar da kashe-kashen, a gudanar da cikakken bincike, tare da kara tsaro a yankin don hana sake aukuwar hare-haren.
Haka kuma, matan sun bukaci agajin gaggawa ga 'yan gudun hijira da rikicin ya raba da gidajensu.
Gwamnan Benuwai ya lallashi masu zanga zanga

Asali: Facebook
Gwamna Hyacinth Alia ya bukaci al’ummar Kwande, musamman matan da ke zanga-zangar, da su kwantar da hankalinsu domin ana kokarin magance matsalar.
Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Sir Kulas Tersoo, ya fitar, gwamnan ya nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa Kwande da Ukum.
Gwamna Alia ya yi alkawarin daukar matakan gaggawa don kare al’ummar yankin, yana cewa ba za a kyale masu aikata wadannan hare-hare ba.
Ya kuma jaddada cewa ba zai yarda wasu su yi amfani da sunansa wajen tayar da rikici ba, yana mai cewa gwamnatinsa na aiki don jin dadin kowa.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda
Mazauna Benuwai sun fara tserewa daga gidajensu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, masu garkuwa da mutane sun kashe wani manomi a garin Akor, jihar Benuwai, duk da karɓar kuɗin fansa daga iyalansa.
Dangin manomin sun biya 'yan bindigar N5.4bn don a sako shi, amma daga bisani aka tsinci gawarsa a wurin da aka ajiye kuɗin fansar.
Fargabar hare-hare na gaba ya sa mazauna Akor da wasu garuruwan makwabta suka fara barin gidajensu domin tsira da rayukansu.
Asali: Legit.ng