Zargin Lalata: Akpabio Ya Yi Fallasa, Ya Fadi Rawar da Marigayi Abba Kyari Ya Taka
- Shugaban Majalisar Dattawa ya ce marigayi Abba Kyari ne ya sa aka cire Joy Nunieh daga mukamin shugabar rikon kwarya a NDDC
- Godswill Akpabio ya ce ya cire Nunieh ne bayan samun wasika daga Kyari da ke zargin ba ta yi bautar kasa ta NYSC ba bayan gama karatu
- Ya musanta zargin cin zarafin da tsohuwar shugabar NDDC ta yi masa, ya ce bayan an cire ta ne ta fara yin wasu ikirari marasa tushe
- Shugaban majalisar dattawan ya ce yana shirin kai Nunieh kotu kan zargin da ta yi masa domin kare mutuncinsa a gaban idon duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya fadi yadda marigayi Abba Kyari ya cire Joy Nunieh daga matsayin shugabar rikon kwarya ta NDDC.
Akpabio ya ce marigayin ne ya yi tasiri wurin cire Joy Nunieh daga muƙamin ba kamar yadda take zarginsa ba har da sharri.

Source: Facebook
An zargi Akpabio da neman mata da lalata
A cewar Akpabio, wanda a lokacin shi ne Ministan Harkokin Yankin Neja Delta, Abba Kyari ya tura masa wasika yana zargin takardun Nunieh ba su inganta ba, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar 2020, Nunieh ta ce ta mari Akpabio ne saboda yunkurinsa na yi mata abin da bai dace ba a gidan bakinsa da ke Apo a birnin Tarayya, Abuja.
Ta ce:
"Me yasa bai fada wa 'yan Najeriya cewa na mare shi a gidansa da ke Apo ba? Na mare shi ne saboda wata dabara da yake son yi."
Akpabio ya fadi dalilin korar Nunieh daga muƙaminta
Akpabio ya ce wasikar ta nuna cewa Nunieh ba ta yi bautar kasa ta dole ta NYSC ba, don haka ya tuntuɓi hukumar don tabbatar da sahihancin batun.
Akpabio ya ce:
"Lokacin da na samu wasikar Abba Kyari da ke cewa takardunta ba su da inganci, na rubuta wa NYSC, da suka amsa, sai na cire ta nan take."
"Bayan an cireta, sai ta fara surutu, da farko ta ce na sa ta rantse, daga baya ta ce na so ta."

Source: Facebook
Akpabio zai shiga kotu kan zargin lalata
Akpabio ya karyata zargin cin zarafin da Nunieh ta yi masa, yana mai cewa zarge-zargen ba su da tushe kuma yana da niyyar shigar da ita kotu.
Ya kara da cewa ba zai yi shiru ba kan wannan zargi, yana mai cewa "hakan ba zai wuce ba," don haka zai shigar da ƙara a kotu cikin sati ɗaya domin bi masa hakkinsa.
Natasha: Sanatocin adawa sun mata alkawari
Mun ba ku labarin cewa Sanata Seriake Dickson ya jagoranci sanatocin jam'iyyun adawa zuwa gidan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Dickson ya ce yana wajen taron gyaran dokokin haraji a ranar dakatar da ita, don haka bai samu damar halartar zaman da aka yi ba amma ya ba ta tabbacin goyon bayansa.
Tsohon gwamnan ya ce majalisa tana da al’adar tallafa wa juna a lokutan wahala, kuma sun yi wa Natasha addu’o’i da shawara don samun mafitar gaggawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

